1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabuwar gwamnatin kawance ta Jamus zata yi tsimin kudi euro miliyan dubu 35

October 25, 2005
https://p.dw.com/p/BvNx

Jam´iyun Christian Union da SPD sun yi kira ga jama´ar wannan kasa da su kara yin shiri wajen tinkarar abin da suka kira gagarumin shirin tsuke bakin aljihun gwamnati. Bayan shawarwarin da suka yi dangane da kafa wani babban kawance a birnin Berlin, shugabar gwamnati mai jiran gado Angeler Merkel da shugaban jam´iyar SPD Franz Müntefering sun ce gwamnatin Jamus ta kuduri aniyar rage yawan kudin da ta ke kashewa da Euro miliyan dubu 35 kafin shekara ta 2007. Ko da yake ba wani bayani dalla-dalla game da matakan yin tsimin kudin da gwamnati ke shirin dauka ba, amma masana harkokin tatalin arziki sun ce kwaskwarimar da za´a yiwa manufofin haraji ba zata kai gaci ba, musamman idan aka yi la´akari da dinbim bashin dake kan kasar.