1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabuwar gwamnatin Palestinu ta samu ƙarbuwa a turai da Amurika

June 18, 2007
https://p.dw.com/p/BuIV

Ƙasashe da ƙungiyoyi daban-daban na dunia naci gabada bayyana goyan baya ga sabuwar gwamnatin Palestinu bisda jagorancin Praministan salam fayyad.

Daga ƙasashen larabawa Masar da Jordan ke kan gaba wajen nuna hadin kai ga wannan gwamnati.

Itama Isra´ila ta yi lale marhabin da gwamnatin tare da alƙawarta fida takunkumin da ta sakawa kudadenPalestinawa.

Ƙungiyar gamayya turai, ta ce lokaci yayi, na bada taimakon kuɗi mai tsoka, ga sabuwar gwmanatin domin tallafa mata, ga ayukan gina Palestinu, haka zalika Amurika da Kanada, da dai sauran ƙasashe masu faɗa aji a dunia.

To saidai ƙungiyar Hamas ta haramta gwamnatin ta Salam Fayyad, ta kumma jaddada Isma´il Haniey a matsayin Pramamistan Palestinu.

A yayin da ya gana da sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Dunia, Praministan Isra´ila Ehud Olmert, da ke ziyara aiki a ƙasar Amurika, ya ambata komawa tebrin shawara da Palestinu, tare da sabuwar gwamnatin.