1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mugabe Parlament

Schaeffer, Ute / DW Afrika/Nahost August 27, 2008

Watani biyar bayan zaɓe,an girka sabuwar Majalisar dokoki a Zimbabwe bisa jagorancin jam´iyar MDC

https://p.dw.com/p/F5o8
Sabuwar Majalisar Dokokin ZimbabweHoto: AP

Bayan taƙƙadamar da aka sha fama da ita, a ƙarshe dai, an girka sabuwar Majalisar Dokokin Zimbabwe watani biyar bayan zaɓe.

Duk da ɗari-ɗari, da kuma adawar da suka nuna, a game da taron ƙaddamar da sabuwar Majalisar Dokokin, a ƙarshe dai ´yan majalisar jam´iyar adawa ta MDC ta Morgan Tchangirai sun halarci bikin.

To saidai sunyi ta kuwa ga shugaba Robert Mugabe a lokacin da ya gabatar da jawabinsa na tsawan mintina 30, wanda kuma aka nuna kai tsaye, a kafofin sadarwa na ƙasa.

Ambata Kalamomi na ɓatanci, kokuma yiwa shugaba Mugabe ihu, tamkar wani juyin juya hali ne, a fagen siyasar Zimbabwe.

A tsawan shekaru 28, da yayi akan karagar mulki, shugaba Mugabe na cin karansa babu babbaka, yana kuma karyawa inda babu gaɓa.

Wannan kuwa ga Mugabe tayi ƙamari a lokacin da ya bayyana cewar an cimma yarjejeniyar girka gwamnati tsakanin Zanu Pf da jam´iyun adawa, abunda ´yan Majalisar suka ce zuƙi ta mallau ce.

Duk da tashe tashen hankulla da kuma barazanar da adawa ke fama da ita a Zimabwe ´yan Majalisar MDC,sun bayyana aniyarsu ta ci gaba da gwaggwarmaya ta hanyar ƙalubalantar Robert Mugabe.

A cikin Majalisar Dokokin,  adawa na da ɗan ƙaramin rinjaye, daga jimlar kujeru 210 ta mallaki 110, saboda haka, Loveno Moyo, na MDC yayi nasara zama shugaban Majalisar Zimbawe.

Wannan shine karo na farko, tun bayan samun ´yancin kan Zimbabwe daga turawan mulkin mallaka, Jam´iyar Zanu Pf ta rasa rinjaye a Majalisar Dokoki.

A halin da ake ciki gwamnatin Robert Mugabe,ta fara tsintar kanta a cikin wani yanayi mai kama da "gawa ta ci ta watse", ta hanyar asara dimɓin magoya baya, domin al´ummar Zimbabwe, na ji a jikinta mumunar tsadar rayuwar da ƙasar ta faɗa ciki da kuma taɓarɓarewar tattalin arziki.

Hatta da sojojin ƙasar, wanda ke bada goyan baya ido rufe, ga shugaba Mugabe, sun fara guna-guni.

Babu shakka MDC ta sami gagaramar nasara, to amma har yanzu akwai sauran rina kaba, ta la´kari da ƙarfin faɗa aji da Mugabe,ke da shi da kuma matsayinsa, na shugaban ƙasa.

Sannan burin shugaban Jam´iyar adawa Morgan Tsvangirai na hawa kan karagar mulki, ya kasa cika, duk kuwa da cewar jam´iyar tayi imani, da ita ta samu nasara  zaɓen shugaban ƙasar da ya wakana.

Shugaba Tabon Mbeki da ya ke jagorantar tawagar shiga tsakanin rikicin siyasar Zimbabwe na da jan namijin aiki  a gabansa, domin bayan kwana da kwanaki na tattanawa, har yanzu an kasa cimma daidaiton girka gwamnatin haɗin kan kasa.

Jam´iysar adawa ta MDC ta samu cikkaken goyan baya daga ƙasashen ƙetare kuma bisa dukkan alamu, ta ɗaura ɗamara cigaba da gwagwarmaya, alal misali, jim kaɗan kamin fara bikin ƙaddamar da Majalisar dokoki, saida ´yan sanda suka cafke wasu ´yan majalisar dokokin MDC.

A halinda ake ciki kuma,MDC ta yi tsaye kanbakanta na cewar mudum Robert Mugabe ya naɗa sabuwar gwamnati ba tare da an cimma yarjejeniya ba, to babu shaka zai gane kurensa.

Ayar tambaya itace shin shugaba Robert Mugabe zai ji wannan jawabi kokuwa za shi zartas da komai, gabansa gaɗe?