1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabuwar takaddama a majalisar dokokin Nijar

November 16, 2016

Gungun 'yan majalisar dokoki a Jamhuriyar Nijar sun gabatar da takardar bukatar gyaran wata ayar sashin kundin tsarin mulki a teburin shugabanta.

https://p.dw.com/p/2Smhe
Sitzung des Parlaments in Niger
Hoto: DW/M. Kanta

Wata sabuwar takaddama ce dai ta kunno kai a cikin majalisar dokokin Jamhuriyar ta Nijar dangane da yunkurin wasu 'yan majalisar dokokin na neman yin gyaran fuska ga wani sashen kundin tsarin mulkin kasa da ya haramta wa shugaban kasa da 'yan majalisa da sauran manyan jami'an gwamnati damar karbar kwangilar gwamnati. 'Yan majalisar dokokin kasar dai na bukatar gyaran aya ta 52 a kundin tsarin mulkin, wadda ke haramtawa shugaban kasa da 'yan majalisa da sauran jami'ai gudanar da kasuwanci ko karbar kwangila daga gwamnati, inda wasunsu ke cewa wannan keta ce kawai.

Sai dai wasu 'yan majalisa da ke goyon bayan wannan sashin na kundin tsarin mulki, na masu ra'ayin cewar wannan tamkar cin amanar kasa ne a bangarensu. Kasancewar da daraja kundin tsarin mulkin ne, majalisar ta cimma hana tazarcen wasu gwamnatoci a baya. Gyaran wani sashi na kundin tsarin mulkin Jamhuriyar ta Nijar din dai na bukatar amincewar kashi uku daga cikin hudu na yawan 'yan majalisa, a yawan kuri'u kuwa ana bukatar akalla kashi hudu daga cikin biyar na wadanda suka kada kuri'ar.