1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

SACE SACEN BAKI A IRAKI.

Zainab Mohammed.October 20, 2004
https://p.dw.com/p/BvfN
Birnin Bagadaza a Iraki.
Birnin Bagadaza a Iraki.Hoto: AP

Yanzu haka dai lamura sun fara dagulewa a kasar Iraki,a dangane da yadda yan yakin sari ka noken kasar ke cigaba dayin garkuwa da yan kasashen waje dake ayyauka nja sake ginin wannan kasa bayan yaki.

Daya daga cikin manya kuma fitattun kungiyoyin agaji na duniya da ake kira Care International,ta dakatar dukkan ayyukanta na agaji a Iraki,kuma tace zata iya ficewa daga wannan kasa,bayan an sace Babban Managan ta.

A jiya nedai aka sace Magret Hassan a cikin garin Bagadaza,kana daga baya a gabatar da ita a zaune ita kadai ta wani kaset na Vedeo ta gidan talabijin,ba tare da bayyana wadanda keda alhakin sace ta ba.

A dangane da hakane babban jamiin kungiyar agajin Geofrey Dennis ya fadawa gidan Radion BBC cewa sun dakatar da dukkan ayyukansu na agaji a wannan kasa.Ya kara dacewa suna da kananan maaikata da dama a Irakin kuma yana cigaba da tuntubansu domin jin halin da ake ciki.

Margret Hassan yar kasar Britania,wadda ta kasance a Iraki na tsawon shekaru 30,ta fada hannun barayin nata ne ,makonni biyu bayan yxan yakin sunkurun Irakin sun fille kann Engineer Kennet Bigley shima dan kasar ta Britania ,acigaba da kamfaign dinsu na yin garkuwa da baki musamman yan yammaci da dasa bomai bomai,wanda ya zuwa yanzu yabar Irakin cikin halin rashin Tabbas tunda Amurka ta jagoranci afka mata da karfin soja a bara.

A hare haren da dakarun Amurkan suka kai a garin falluja a daren jiya dai sun kashe wani dan Iraki da matarsa da yayansu 4.Wadanda suka ganewa idanunsu wannan harin sun bayyana yaddda aka tono gawawwakin wannann iyali na mutum shida ,sakamakon harin na sojin Amurka.Ayayinda dakarun Amurkan suka nuni dacewa suna kai hare haren daren da nufin afkawa magoya bayan dan kasar Jordan din nana da Amurka ke nema ruwa a jallo Abu Musab al-Zarqawi,mutuminda kuma suke zargi da kasancewa a garin na Falluja,mai tazarar km 50 yammacin birnin Bagadaza.Sai dai mazauna garin na falluja sun hakikance cewa basu da masaniya dangane da wannan bawan Allah da ake nema,wanda kuma hakan ya sanaya mazauna garin ke rayuwa cikin tashin hankali saboda irin asaran rayuka da akeyi a kowane wayewan gari,ba tare da anji kamshin wanda ake nema ba.

A garin Baquba dake arewacin Bagadaza kuwa,wani matashi mai shekaru 15 da haihuwa ya gamu da ajalinsa sakamakon tashin boma bomai biyu da aka dasa gefen kusa da ayarin motocin Amurka.Bomb din dai ya raunana Dakarun Amurkan biyu.Ayayinda wasu yan bindiga dadi kuma suka kashe wani dankwangilan Iraki dake aiki wa Dakarun Amurkan a garin na Baquba.

Rahotanni daga Bagadazan kuwa na nuni dacewa wasu yan bindiga dadi sun harbe mai bawa Prime ministan Irakin Iyad Alawi shawara kann harkokin siyasa.Ayayinda Yan yakin sunkurun na Iraki ke gargadin gwamnatin koriya ta kudu data janye dakarun ta 2,800 dake Irakin ko kuma su afkawa babban birnin kasar Seoul.Daga watan Afrilu zuwa yanzu dai yan kasashen waje da dama aka sace da yin garkuwa dasu a Irakin,a kalla 35 daga cikinsu kuwa sun bakunci lahira ta hanyar ta hanyar fille kawunansu.