1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

sadam na yajin cin abinci

June 22, 2006
https://p.dw.com/p/Bu6R

Tsohon shugaban kasar Iraki Sadam Hussein ya shiga yajin cin abinci ,sakamakon kisan gilla da akayiwa daya daga cikin lauyoyi dake kareshi.To sai dai sojojin Amurka dake tsare da da sadam da sauran jamian gwamnatinsa,sun bayyana cewa tsohon shugaban Iraki baya cikin masu yajin cin abincin.

Shugaban tawagar Lauyoyin Sadam Khalil al-Dulaimi ya bayyana cewa ,shi da sauran jamiai 55 dake tsare ,sun fara wannan bore na zama da yunwa ne ,bayan sun samu labarin kashe Khamis al-obeidi a jiya laraba,wanda ke zama lauya na uku dake kare wadanda ake karan,da fara zaman sauraron shariar sadam a watan oktoban daya gabata.

Da sanyin safiyar jiya nedai wasu mutane sanye da kayan sojin Iraki ,suka sace obeidi mai shekaru 49 da haihuwa daga gidansa,wanda daga baya aka tsinci gawarsa a kann titi a bagadaza.