1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Saddam Hussain ya shiga yajin kin cin abinci

February 14, 2006
https://p.dw.com/p/Bv83

A kasar Iraki, a na ci gaba da shari´ar tsofan shugaban kasa Sadam Hussain, tare da wasu mutane 7.

A yau Saddam, ya bayana cewa, tun kwanaki 3 da su ka wuce ya fara yajin kin ci abinci.

A na tuhumar su, da kissan mutane 148 a garin Duja´il ,a shekara ta 1982.

Saddam Hussain, bai bada dallilan da su ka shi, shiga yajin kin cin abinci ba.

A ci gaba kuma, da kai hare haren a wannan kasa,a yamancin jiya , an hallaka shugaban rundunar bada horron yan sanda, na birnin Bagdaza.

Sannan a sahiyar yau, wata bom ta fashe , inda ta yi sanadiyar jimuwar yan sanda guda 2.

Kazalika, ministan harakokin tsaro ya sannar cewa, an gano gawawakin mutane 4, a wuraren daban daban na Birnin Bagadaza tun da sanhin sahia.

Bugu da kari, wani mai yi wa rundunar sojojin kasar Hidima ya rasa ransa, bayan da wasu yan kunar bakin wake, su ka haka masa, harin kwantan bauna.