1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Saddam Hussain yace ba zai sake halartar kotun dake tuhumar sa ba

December 6, 2005
https://p.dw.com/p/BvHf

Tsohon shugaban kasar Iraqi wato Saddam Hussain yace mahukuntan kasar Amurka da israela na daga cikin sahun gaba na ganin ya rasa ransa.

Tsohon shugaban na Iraqi ya fadi hakan ne kuwa yayin da yake mayar da martani game da abin da wata mata ta fadawa kotun da cewa an take mata hakki a lokacin zamanin mulkin tsohon shugaban na Iraqi.

Saddam Hussain yaci gaba da shaidawa kotun cewa daga kansa izuwa magoya bayan sa babu wanda yake tsoron ya rasa ransa a wannan hali da suke ciki.

Rahotanni dai sun nunar da cewa kusan dukkannin wadanda suka bayar da shaidar a yau sunyi hakan ne , bayan da aka kange su da wani labule da ba a ganin su a fili a saboda hali na tsaro.

Bayanai dai sun shaidar da cewa tsohon shugaban na Iraqi da mukarraban nasa na fuskantar zargi ne na kisan bayin Allah 148 a shekara ta 1982.

Wannan dai kisan kiyashi an aiwatar dashi ne a garin Dujal bayan wani yunkuri da akayi a garin na kisan tsohon shugaban kasar ta Iraqi.

A kuwa yayin da kuwa kotun ke tunanin dage zaman ta , Saddam hussain cikin fushi yace ba zai kara zuwa halartar zaman kotun ba bisa rashin adalcin daya kira ke wakana a cikin zaman kotun.An dai dage zaman wannan kotu a yammacin na yau izuwa gobe laraba idan Allah ya kaimu