1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Saddam zai fuskanci sabon zargi na kisan kiyashi

April 4, 2006
https://p.dw.com/p/Bv34

Kotun dake sauraron karar shari´ar Saddam da mukararraban sa, tace a nan gaba kadan za a fara sauraron shari´ar zargin da akewa tsohon shugaban kasar na Iraqi a game da kisan kiyashi daya faru a garin Anfal.

Rahotanni dai sun nunar da cewa za a gurfanar da Saddam ne tare dana hannun daman sa guda 7 a game da wannan sabon zargi daya taso.

Mai gudanar da bincike a game da hakan wato alkali Raed Al Juhi, tuni ya tabbatar da cewa bincike a game da hakan ya kammala , tuni ma ya mika rahoton sa ga kotu don fara sauraron wannan shari´a.

A cewar mai gabatar da kara, wato Jaafar Al Mussawi, ana zargin Saddam Hussain nin ne da mukarraban nasa da laifin yin kisan kiyashi ga kurdawan yankin na Anfal tare kuma da rushe gidajen mutane dubu 4 da dari biyar a shekara ta 1987 izuwa 1989.