1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Saddama zai sake baiyana a kotu

August 21, 2006
https://p.dw.com/p/Bum4

Tsohon shugaban ƙasar Iraqi Saddam Hussaini tare da mukarraban sa su shida waɗanda suka haɗa da ɗan uwan sa Ali Hassan al-Majid wanda aka fi sani da Chemical Ali a yau za su sake gurfana a kotu a tuhumar da ake musu ta farmakin soji da aka yiwa laƙabi da Anfal wanda ya yi sanadiyar mutuwar dubban jamaá da kuma ƙone ƙauyuka kimanin 2,000. Ana zargin sojin ƙasar a zamanin mulkin Saddam da yin amfani da sinadarin iskar gas mai guba don hallaka dubban kurɗawa da suka haɗa da mata da ƙananan yara a ƙauyen Halabja a shekarar 1988. Saddam da dan uwan sa Majid ana tuhumar su ne da kisan ƙare dangi yayin da sauran muƙarraban na sa huɗu ake tuhumar su da aikata laifukan yaki.