1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakamakon Binciken Kungiyar OECD

September 14, 2004

A yau talata kungiyar OECD ta gabatar da sakamakon bincikenta a game da matsayyin ilimi a kasashe 26 dake da ci gaban masana'antu a duniya.

https://p.dw.com/p/BvgU

Rahoton na kungiyar hadin kan tattalin arziki da al’amuran rayawa ta OECD ya kunshi shafi sama da 500. Rahoton wanda ya tanadi nazarin da aka gudanar tsakanin shekarar 1995 zuwa shekara ta 2001, wanda aka gabatar da shi karkashin taken:"ayanin tsarin ilimi a dunkule", ya jibanci kasashe 26 da aka kwatanta tsare-tsarensu na ilimi da juna. A karkashin rahoton Jamus ta samu mummunan koma baya daga matsayi na 14 zuwa matsayi na 20, duk kuwa da cewar kasar ta bunkasa yawan abin da take kashewa a harkar ilimi da misalin kashi 7%. To sai dai kuma ragowar kasashen kungiyar ta OECD sun yi karin abin da ya kai kashi 30%. Amma duk da wannan gagarumin gibin wakilin Jamus a tsakanin tawagar kwararrun na kungiyar OECD da suka gudanar da wannan bincike ya yaba wa kasar da taka rawar gani a cikin shekarun baya-bayan nan, musamman wajen kara yawan makarantun jeka-ka-dawo a ko da yake har yau da sauran rina a kaba dangane da makarantun faramare da na renon yara kanana. Wani abin da wakilin na Jamus Andreas Schleicher yayi madalla da shi kuma shi ne ci gaban da aka samu a game da manyan makarantu na gaba da sakandare. A cikin shekaru biyar din da suka wuce an samu karuwar yawan dalibai a jami’o’in kasar daga kashi 28 zuwa kashi 35% na wadanda ake yayewa daga makarantun sakandare a shekara. Ministar ilimi ta Jamus Edelgard Bulmahn ta bayyana gamsuwarta da sakamakon binciken na kungiyar OECD inda tayi nuni da cewar an yi karin abin da ya kai kashi 36% a harkar ilimi a nan kasar tun abin da ya kama daga 1998 zuwa yanzun. Ta ce wani abin lura musamman dangane da tattalin arzikin Jamus dake ba da fifiko ga cinikin ketare shi ne kasancewar kimanin kashi daya bisa uku na daliban da ake yayewa daga jami’o’in kasar injiniyoyi ne ko kuma masana kimiyya. A wannan bangaren Jamus ce a matsayi na biyu a tsakanin kasashen OECD su 26 dake da ci gaban masana’antu. A baya ga haka an samu karuwa ta kashi 72% na dalibai a fannin kimiyya da fasaha tun abin da ya kama daga shekara ta 1998 sai kuma karin kashi 35% na injiniyoyi. Shi ma ministan ilimi na jihar Brandenburg Steffen Reiche yayi madalla da sakamakon binciken wanda a ganinsa yake nuna gagarumin ci gaban da Jamus ta samu bisa manufa. Ya ce sannu a hankali ne kasar zata sake farfadowa domin komawa matsayin da aka santa a da. Kasashe kamar Sweden da Finland sai da suka yi kimanin shekaru 25 suna lalube a cikin dufu kafin su durfafi wata alkibla madaidaiciya a game da manhajojinsu na ilimi. A dai wannan marra da ake ciki yanzu haka kasar Koriya ta Kudu ta fi kowace kasa kashe kudi a harkar ilimi a tsakanin kasashen OECD inda take kashe abin da ya kai kashi 8‘5% na kasafin kudinta a harkar ilimi. Wannan kasa, kamar yadda Andreas Schleicher ya nunar, ta kasance daidai da kasar Afghanistan a matsayi na ilimi a cikin shekarun 1960.