1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakamakon bukuwan tunawa da ran 11 ga watan Satumba

YAHAYA AHMEDSeptember 12, 2006

Bayan gama bukuwan juyayin da aka yi ta yi, musamman a Amirka, don tunawa da waɗanda suka rasa rayukansu a harin ƙunan baƙin waken ran 11 ga watan Satumban shekrara ta 2001, ina aka nufa? Wai shugaba Bush ya koyi wani darasi daga waɗannan hare-haren kuwa? Ko kuwa zai yi ta janyo wa Amirka baƙin jini ne da manufarsa ta yaƙi da ta'addanci?

https://p.dw.com/p/BtyE
Juyayin ran 11 ga watan Satumba a birnin New York.
Juyayin ran 11 ga watan Satumba a birnin New York.Hoto: picture-alliance/dpa

Bukukuwan da aka yi na cika shekaru 5 da kai harin ƙunan baƙin waken nan na ran 11 ga watan Satumba a Amirka, na tunasad da mutane ne da irin asarar rayukan da aka yi a wannan ranar a cikin shekara ta 2001. Tashoshin tlabijin da dama kuma ne suka yi ta nuna hotunan wannan annobar.

Shugaban Amirka, George W. Bush, ya yi amfani da wannan damar wajen yi wa al’umman ƙasarsa jawabi a kan talabijin, inda ya yi ta nanata cewa, ƙasarsa ta sami kanta cikin yaƙi ne saboda ƙalubalantar da aka yi mata. Kuma babu shakka Amirkan ce a ƙarshe za ta sami nasara. Makomar duniya dai ta dogara ne kan cin nasarar wannan yaƙin, inji shugaban. Amma masharhanta da dama kamar dai Felix Steiner, na ganin cewa, irin waɗannan kalamun ne ke ƙara dusashe kwarjinin Amirkan a ƙetare.

Har ila yau dai shugaba Bush bai iya ya ba da amsar tambayar da ake ta yi a ko yaushe, game da dalilin da ya sanya Amirka afka wa Iraqi da yaƙi ba. Yanzu kam ko wa ya sani a zahiri cewa, Saddam Hussein ba shi da wata jiɓinta da harin ƙunan baƙin waken ran 11 ga watan Satumba. Sabili da haka, babu abin da ke hujjanta kai wa ƙasarsa hari wai don yaƙan ta’addanci.

Da kamata ya yi dai, shugaban Amirkan ya shiga cikin wani dogon tunani a kewayowar ran 11 ga watan Satumban, a karo na biyar. Ya kuma yi la’akari da martanin da ake ta mayarwa a ƙasashen larabawa. A lokacin harin dai ƙasashen Gabas Ta Tsakiya da dama ne suka nuna zumunci ga Amirka, saboda ɗimbin yawan asarar rayukan da aka yi. To amma a yau, ko ambatar wannan harin ba a yi a muhimman kafofin yaɗa labaran yankin. A daura da haka, abin da ke jan hankullan kafofin ne halaka mutanen da ake ta yi a ko wace ranar Allah a ƙasar Iraqi. Babu kuma abin da ya janyo wannan halin face afka wa ƙasar da Amirkan ta yi. A baya-bayan nan kuma, mutane fiye da dubu ne suka rasa rayukansu sakamakon hadarin bamabaman da Isra’ila ta yi wa ƙasar Lebanon, tare da ɗaurin gindin Amirka. Har ila yau dai, ba za a iya mantawa da gallazawa da wulakantad da fursunonin Iraqin da aka yi a gidan yarin Abu Ghraib ba, ko kuma batun sansanonin sirrin nan na ƙungiyar leƙen asirin Amirka wato CIA inda ake take hakkin fursunoni, wai don yi musu tambayoyi. Ga kuma sansanin Guantanamo Bay a Kuba, inda har ila yau ake tsare da ɗimbin yawan mutane ba tare da an ɗaukaka ƙara game da su ba. To wane ne kuwa, idan dai yana cikin hankalinsa, ba zai gane cewa munafunci Amirka ke yi ba? Ta hakan dai babu yadda za a yi a yaƙi ta’addanci.

Yanzun dai lokaci ya zo da ya kamata shugaba George W. Bush na Amirka ya yi la’akari da abokan burminsa. A lokacin da aka kai harin a cikin shekara ta 2001 dai, duk ƙasashen Turai da na ƙungiyar NATO sun nuna masa cikakken goyon baya. To amma yau fa? Tuni dai yaƙin Iraqi ma ya janyo ɓaraka tsakanin mambobin ƙungiyar. Ko riƙaƙƙun abokan burminsa, shugaban gwamnatin tarayyar Jamus Angela Merkel da ministan harkokin cikin gidanta Wolfgang Schäuble ma na ɗari ɗari da manufofinsa. Bayan juyayin da aka yi a ran 11 ga watan Satumban dai, kamata kuma ya yi a sake nazarin manufar Amirkan ta yaƙan ta’addanci, don a iya gano cewa salon da take bi ba hanyar da ta dace ba ne.

A ziyarar da ya kawo a ƙasar haihuwarsa, wato nan Jamus, Papa Roma Benedict na 16, ya yi matashiya da wannan salon, amma ba tare da ambatar wata ƙasa ba, inda ya yi kira ga girmama duk al’adun da wasu ke ɗauka da muhimmanci. A kuma guji wulakanta waɗannan al’adun. Da dai Amirkawan za su yi aiki da wannan shawarar, da za a iya kaucewa daga kurakurai da yawa, musamman a manufar da suka sanya a gaba wai ta yaƙan ta’addanci.