1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afirka ta Kudu: Jam'iyyar DA na gaba

Lateefa Mustapha Ja'afarAugust 5, 2016

A karon farko cikin shekaru 20 da ta kwashe tana mulki a Afirka ta Kudu, jam'iyyar ANC na shirin shan gagarumin kaye a zaben kananan hukumomi da aka gudanar a kasar.

https://p.dw.com/p/1Jbxj
Shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma da jam'iyyarsa ke shirin shan kaye a zabe.
Shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma da jam'iyyarsa ke shirin shan kaye a zabe.Hoto: Reuters/N. Bothma

Sakamakon farko na kuri'un da aka rigaya aka kidaya da rahotanni ke bayyana cewa sun kai kaso 98 cikin 100 na baki dayan kuri'un da aka kada, na nuni da cewa jam'iyyar ANC ta Shugaba Jacob Zuma na da kaso sama da 40 cikin 100 yayin da jam'iyyar adawa ta Democratic Alliance DA, ke da kaso 46 cikin 100. Manazarta dai na alakanta sakamkon zaben da irin halin kunci musamman ma na rashin aikin yi a kasar, da suka janyo bakin jini ga Shugaba Zuma. Jam'iyyar Zuma ta ANC dai ta rasa manyan biranen kasar da dama da a baya ke hannunta ciki kuwa har da Pretoria baban birnin kasar, inda jma'iyyar DA ta samu rinjaye. Wannan dai na sanya hasashen cewa ta yi wu jam'iyar ta ANC ta sha kaye a babban zaben kasar da ke tafe, wanda za a gudanar a shekara ta 2019.