1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakamakon farko na zaben shugaban ƙasa a Sudan

April 16, 2010

Sakamakon farko na wasu gundumomi a Sudan na nuni da cewa shugaba al Bashir shine akan gaba.

https://p.dw.com/p/Mym0
Shugaban ƙasar Sudan Omar Hassan al-BashirHoto: AP

Sakamakon farko dake fitowa a zaɓen farko a ƙasar Sudan bisa tafarkin Jamíyu da dama na nuni da cewa shugaban ƙasar mai ci na kan gaba. Dama dai an tsammaci shugaba Omar al-Bashir zai sami nasarar yin tazarce na wasu shekaru biyar a karagar mulki bayan da babban ɗan takarar dake ƙalubalantarsa ya janye daga zaɓen bisa hujjar rashin halasci.Sakamakon zaɓen wasu gundumomi da hukumar ta baiyana ya nuna al-Bashir ya sami tsakanin kashi 88 zuwa kashi 94 cikin ɗari na ƙuriún da aka ƙidaya. Ana sa ran samun cikakken sakamakon zaɓen a ranar Talata mai zuwa. Zaɓen dai na daga cikin muhimman ƙudirorin da aka amince dasu a yarjejeniyar da aka sanyawa hannu a shekarar 2005 tsakanin arewaci da kudancin ƙasar wanda kuma zai share fagen kaɗa ƙuriár raba gardama a shekara mai zuwa wanda zai bada damar yancin cin gashin kai ga kudancin ƙasar ta Sudan.

Mawallafi : Abdullahi Tanko Bala

Edita       : Zainab Mohammed Abubakar