1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakamakon taron London kan Afghanistan

Umaru January 29, 2010

Kasashen yamma sun yi alkawarin taimako ga Afghanistan yadda gwamnmati a Kabul zata karbi mulkin kasar da kanta

https://p.dw.com/p/Llbq
Shugaban Afghanistan Hamid Karsai a taron LondonHoto: AP

Kasashen yamma sun baiyana niyyar su ta jan hankalin mayakan kungiyar Taliban, ta hanyar taimakon kudi, domin tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a kasar Afghanistan, yadda hakan zai bada damar mika aiyukan da kullum na kasar zuwa ga gwamnati a Kabul. A lokacin taron London da kasashen da yamma suka shirya kan Afghanistan, Pirayim ministan Ingila, Gordon Brown ya yayi magana game da abin da ya kira, kafa tushen wa'adi kafin kasar ta koma hanun gwmanatin ta. Umaru Aliyu yana dauke da karin bayani.

Taron Afghanistan da aka yi a London ranar alhamis, an kare shi ne tare da alkawura da dama, na bullo da wani sabon tsari kan wannan kasa. Wannan sabon tsari kuwa shine, mika Afghanistan ga yan Afghanistan. Kasashen da suka halarci taron sun daidaita kan bukatar ganin sannu a hankali an mika aiyukan tsaro da na farar hula zuwa ga ita kanta gwamnatin Afghanistan. Wadannan kasashe suna kuma da burin ganin cewar wannan shiri, akalla bangaren da ya shafi soja, an kare shi nan da shekaru biyar masu zuwa.

Babban sakon dake kunshe a taron na London shine: bama bukatar sake maimaita kura-kuran da muka yi da can kan Afghanistan. Mai masaukin baki, Pirayim minista Gordon Brown na Ingila, maimakon haka, yayi magana game da sabon tsari da hanyoyi masu yawa da za'a bi, domin kawar da barazanar al-Qaeda a Afghanistan. Brown ya kwatanta taron na London ne a matsayin wani kafa sabon tushe na kokarin shawo kan wannan rikici.

Yace wannan taro ya shimfida sabon zamani na zaman wa'adi. Zamu mika alhakin kula da tsaro daga lardi zuwa lardi daga jiha zuwa jiha zuwa ga jami'an tsaro da yan Afghanistan.

Pirayim ministan na Ingila yace za'a baiwa jami'an tsaron na Afghanistan taimakon kudi mai yawa. Nan da shekaru biyu masu zuwa, Afghanistan zata kasance da sojoji dubu dari da saba'in da yan sanda dubu dari da talatin. Brown ya kuma kare shirin tura karin sojoji dubbai na Ameriia da na Ingtila zuwa Afghanistan. Yace matsin lambar soja, ita ce hanyar da ta dace sakamakon hare-haren da yan ta'adda suke yi. A lokaci guda, ya kuma mikawa yan kungiyar Taliban hannun sulhu. Duk dan Taliban da yayi watsi da makaman sa, yana iya cin gajiyar waniu shiri na taimakon wadanda suka janye daga kungiyar.

Shugaba Hamid Karsai, wanda ya nuna gamsuwar sa da sakamakon taron, ya ma yi alkawarin kiran zaman taron majalisar dokokin Afghanistan, Loya Jirga a takaice, nan da watanni ukku masu zuwa, domin tattauna batun zaman lafiya.

Yace a kokarin tabbatar da samun nasarar shirin na zaman lafiya, zamu nemi gudummuwa da taimako daga Sarkin Saudi Arabia. Zamu kuma nemi taimako daga makiwabtan mu, musamman Pakistan, su goyi bayan kokarin mu na zaman lafiya.

Ministan harkokin wajen Jamus, Guido Westerwelle, ya sake maimaita bukatar kasashen yamma na tabbatar da ganin an kiyaye hakkin yan Adam a Afghanistan. Shi ya baiyana gamsuwa da sakamakon taron na London.

Yace wannan taro a nan London hakika ya zama na kafa sabon tushe, kuma mu Jamusawa muna iya fadin fadin cewar mun bada gudummuwa, saboda mun taimaka domin ganin an kai ga sakamakon da ya samu.

Westerwelle yace ko da shike kasashen duniya da ska halarci taron sun nemi karin kudi, amma Jamus bata yi wa kasar alkawarin kudin da bashi da iyaka ba. Maimakon haka, zamu nemi shugaba Karsai ya cika alkawarin da yayi na tafiyar da mulki na-gari da yaki da cin rashawa.

A zauren taron, shi kansa Hamid Karsai yayi sukan ganin cewar kashi 80 cikin dari na taimakon kudi da ake yiwa kasar sa alkawari, ba'a baiwa gwamnatin sa kai tsaaye.