1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakamakon wucin gadi na zaɓen shugaban ƙasa a DRC

August 17, 2006
https://p.dw.com/p/BumP

Al´ummomin Jamhuriya Demokradiyar Kongo, na ci gaba da jiran sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da na yan majalisun dokoki da aka gudanar, ranar 30 ga watan juli da ya wuce.

Ya zuwa yanzu, hukumar zaɓe mai zaman kanta, ta bayyana kusan kashi 50 bisa 100, na jimmilar ƙuri´un da a ka kaɗa.

Har yanzu, shugaban ƙasa Joseph Kabila, ke sahun gaba, tare da kussan kashi 52 bisa 100 , to saidai, idan a ka kwatanta da sakamakon ƙuri´un da ya samu, a farkon wannan mako, an samu ragowar tazara tsakanin sa da sauran yan takara.

Ɗan takarar da har yanzu ke sahu na 2, wato Jean Pierre Bemba, ya tattara kashi 15 bisa 100.

Kawo yanzu, babu wani bayani, a game da sakamakon zaɓen Kinshasa, birnin da ya ƙunshi kashi 12 bisa 100, na yawan jama´ar da su ka jefa ƙuri´u.