1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakamakon zaɓen shugaban ƙasa a Sudan

April 26, 2010

Umar Hasan El-Bashir ya sami damar yin tazarce a shugabancin ƙasar Sudan.

https://p.dw.com/p/N6zm
El Bashir ya lashe zaɓeHoto: AP

Shugaba Umar Hasan El Beshir na Sudan yayi nasarar lashe zaben shugabancin ƙasa da ya gudana makwani biyun da suka gabata. Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ya baiyana cewa El Bashir ya lashe kashi 68 da digo 24 daga cikin 100 na ƙiru´un da aka kaɗa. Tun bayan da fitattun yan siyasan ƙasar ta Sudan suka janye takararsu bisa zargin magudin zabe ne, aka tabbatar da cewa babu makawa Umar Hasan El-bashir zai sami damar yin tazarce. Cikin jawabin da yayi wa yan Sudan jim kadan da baiyana sakamakon, El Bashir yayi alƙawarin mutunta jadawali da aka tsaida na shirya zaben jin ra´ayin jama´a a kudancin Sudan a watan janairun badi. Kotun hukunta manyan lafukan yaƙi da cibiyarta ke birnin Hague ta miƙa sammace domin a kama El Bashir da ya shafe shekaru sama da 20 a kan karagar mulkin Sudan.

 Mawallafi: Mouhamadou Awal 

Edita: Mohammad Awal