1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakamakon zabe a Sierra Leon

August 12, 2007
https://p.dw.com/p/BuEG

Bayan gudaanar da zaben shugaban kasa dana yan majalisa a jiya a kasar saleon,a halin yanzu haka an fara gudanar da kidayan kuriu da aka kada.Zaben wanda ke zama na farkon irinsa tun bayan janye dakarun kiyaye zaman lafiya na mdd daga wannan kasa,na mai zama zakaran gwajin dafi fitowar kasar ta Saleon daga shekaru na yakin basasa.Masu sa idanu na kungiyar tarayyar turai dai sun bayyana gamsuwarsu da yadda zaben ya gudana.

A yanzu haka kuma ana cigaba da gudanar da kidayan kuriun cikin lumana,koda yake an tura jamian tsaro suna sintiri cikin birnin Freetown,adangane da barazanar da wasu mata sukayi na kawo cikasa a harkokin kidayan.Anasaran shugaban jammiyyar adawa ta APC Ernest Koroma,zai kalubalanci mataimakin shugaban kasa Solomon Berewa , akan wannan mukami na shugabancin wannan kasa ta Saleon dake yankin yammacin Afrika.