1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakamakon zabe na Tanzania

Hauwa Abubakar AjejeDecember 19, 2005

Sakamakon zaben shugaban kasa da aka baiyana ya nuna cewa,Jamiyar dake mulki a kasar Tanzaniya tun samun yancin kanta shekaru fiye da 40 da suka shige, ta samu nasarar ci gaba da mulkin kasar,bayan dan takararta ministan harkokin waje,Jakaya Kikwete ya lashe zaben.

https://p.dw.com/p/Bu3I
Jakaya Kikwete
Jakaya KikweteHoto: DW

Kikwete dan shekaru 55,ya samu kwashe kashi 80 cikin dari na kuriu daaka kada a zaben da aka gudanar ranar laraba,inda ya kayarda yan takara 9 a zaben kasar karo na uku tun kaddamar da siyasa mai jamiyu fiye da daya a kasar a 1992.

Hakazalika jamiyarsa ta CCM ta samu rinjaye a zaben majalisar dokoki.

Kikwete zai gaji shugaba Benjamin Mkapa,wanda tsarin mulkin kasar ya dakatar da shi daga sake tsayawa takara karo na uku a matsayin shugaban kasar.

Yan takara da suka sha kaye sun hada da,Ibrahim Lipumba wanda ya samu kashi 11 da rabi cikin dari na kuriu,sai Freeman Mbowe wanda ya samu kashi kusan 6 bisa dari da kuma Augustine Mrema na jamiyar TLP.

Kashi 72 cikin dari na wadanda suka cancanci jefa kuria su miliyan 16 da dubu 300 ne suka kada kuriunsu,cikin zaben da ya gudana cikin lumana a kasar,kodayake an samu yan fitunu a tsibirin Zanzibar dake karkashin Tanzania,inda mutane 20 suka samu rauni tare kuma da tsare wasu da dama.

Har yanzu ana cikin halin dar dar a karamin tsibiri na Tumbatu,inda magoya bayan jamiyun CCM da CUF suka kara suna masu zargin magudi a zaben.

Jamiyar CCM wadda tayi mulkin kasar tun samun yancin kanta daga hannun Burtaniya a 1961,ta kuma lashe zaben shugaban kasa da na yan majalisa a tsibirin Zanzibar dake karkashinta cikin zarge zarge na magudi da jamiyar CUF tayi mata.

A zaben majalisar dokoki jamiyar dake mulkin ta kwashe kujeru 206,idan aka kwatanta da kujeru 19 da jamiyar adawa ta CUF ta samu,jamiyar CHADEMA kujeru 5 sai kuma kujeru dai dai ga jamiyun TLP da kuma UDP.

Dukkannin kujeru da babbar jamiyar adawa CUF ta samu sun fito ne daga tsibirin Zanzibar inda tafi karfi.

Jamiyun adawa dai tun farko sunyi anfani da matsalolin cin hanci da karbar rashawa,talauci da rashin aikin yi da suka addabi jamaa wajen yekuwar neman zabe da sukayi a manyan garuruwa da biranen kasar,inda mafi yawa na jamarta miliyan 35 suke zaune.

Yan adawan sun zargi Kikwete wanda yake da goyon bayan shugaba mai barin gado Mkapa, da laifin yin anfani da albarkatun kasar wajen yakin neman zabensa.

Fiye da rabin jamaar kasar da kuma kusan kashi 80 cikin dari na maaikata sun dogara ne akan aikin gona,wanda har yanzu ya gagara farfadowa daga shiryukan bunkasa noma da tsohon shugaba dan kishin kasa Julius Nyere ya bullo da su.

Shugaba Nyerere,wanda yayi mulkin Tanzania daga 1961 zuwa 1985 ya rasu ne 1999.

Kasar ta Tanzania dai tayi shekaru 31 bayan samun yancinta karkashin mulkin jamiya daya tilo ta CCM.

Amma abubuwa sun canza a 1992,a lokacinda magajin Nyerere,Ali Hassan Mwinyi,ya bada damar kafa jamiyun siyasa fiye da daya,tare da gudanar da zabuka shekaru uku da suka biyo baya.

Cikin shekaru 10 da yayi yana mulki,Mkapa,ya kusa kai kasar ga tsarin kasuwanci na zamani,inda yayi ta samun yabo daga masu bada lamuni na kasa da kasa,amma kuma ya tsarin ya sanya yawancin jamaarsa cikin talauci.

Sabon shugaban,Kikwete,yayi alkawarin ci gaba da bin manufofin shugaba mai barin gado Benjamin Mkapa.