1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakamakon zaben majalisa a Bahrain

November 27, 2006
https://p.dw.com/p/Bua1

Yan darikar Shia masu rinjaye a masarautar Bahrain sun samu nasaran tofa albarkacin bakinsu cikin harkokin siyasar kasar dake karkashin sarautar yan darikar Sunni,a karon farko,sakamakon zaben majalisar dokoki daya gudana a ranar asabar data gabata.Jammiiyar Al-Wefaq na shiawan kasar ,dake zama kungiyar adawa mafi girma ta lashe kujeru 16 daga cikin 17 datayi takara,daga cikin adadin kujeru 40 na majalisar dokokin Bahrain .Sai dai shugaba Kungiyar ta Wefaq Shekh Ali Salman,yayi watsi da yiwuwar wani sauyi adangane da harkokin siyasar kasar,bisa laakari da majalisar Shura mai wakilai 40 da aka nada,wadanda kuma sune kadai da Sarki Hamad bin Isa al-Khalifa,zasu iya amincewa da kowace irin doka.