1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakamakon zaben Masar

September 12, 2005

Tare da rinjayen sama da kashi 80% shugaba Mubarak ya cinye zaben kasar Masar mai 'yan takara barkatai

https://p.dw.com/p/BvZk
Shugaba Mubarak na Masar
Shugaba Mubarak na MasarHoto: AP

Wani dan kasar ta Masar dai ya fada a cikin ba’a cewar ba za a iya kwatanta wani zaben da mai nasararsa zai tashi da kashi 80% na jumullar kuri’un da aka kada tamkar zabe na demokradiyya ba. Ta la’akari da haka kuwa ana iya cewar ko da yake kasar Masar ba ta rungumi mulkin demokradiyya ba, amma ta durfafi wannan alkibla. Duk dai wanda ya waiwayi baya zai ga cewar a watan oktoban 1987 lokacin da shugaba Mubarak ya bari aka sake zabensa domin wani sabon wa’adin mulki na shekaru shida, an yi kirarin cewar shugaban ya samu goyan bayan kashi 97.1% na jumullar kuri’un da aka kada. Amma a shekara ta 1993 sai alkaluman suka tsaya akan kashi 96.3%, sannan a 1999 ya samu goyan bayan kashi 94% kacal. A kuma zaben na baya-bayan nan Mubarak ya tashi ne da kashi 88.5%. To sai dai kuma abin lura a nan shi ne kasancewar duka-duka kashi 23% na masu ikon kada kuri’a su miliyan 32 ne suka halarci zaben, inda a karon farko a tsakanin kasashen Larabawa aka samu wasu ‚yan takara dake kalubalantar shugaba mai ci a zabe. Kuma kamar a zabubbuka na baya, a wannan karon ma ba za a iya cewar zaben ya tafi salin-alin ba tare da magudi ba duk da ikirarin da aka yi a hukumance, inda ‚yan hamayya suka yi nuni da dabaru daban-daban na magudi, kamar dai kada kuri’a sau biyu da rashin sahihan matakai na sa ido da kuma hana magoya bayan ‚yan hamayyar kada kuri’unsu. A sakamakon haka dan takara mai farin jini tsakanin jama’ar kasar Masar Ayman Nour ya tashi da kashi 7% sannan ragowar ‚yan takarar baki dayansu suka cimma kashi daya bisa bakwai na jumullar kuri’u miliyan bakwai da aka amince da ingancinsu. To sai dai kuma duk da wannan korafin tun da farko aka hakikance da gaskiyar cewar Mubarak ne zai cinye zaben, saboda a kasar ta Masar maganar zabe na demokradiyya jaririya ce kuma ba a santa sosai ba. A baya ga haka da yawa daga al’umar kasar na tattare da imanin cewar babu wani abin da zai canza, Ya-Allah sun shiga zaben ko kuma sun kaurace masa, duk kuwa da cewar kimanin kashi 53% ne suka shiga kuri’ar raba gardama da aka kada a ‚yan watannin da suka wuce akan canje-canje ga dokokin zabe da kuma amincewa da ‚yan takara barkatai. Akalla dai abin da za a iya cewa a takaice shi ne kasar Masar ta durfafi wata alkibla mai muhimmanci. Kazalika shi ma zargin magudin zaben a bainar jama’a, shi ma wani sabon lamari ne, ba ma a Masar kadai ba, har da sauran kasashen Larabawa. A kuma halin da ake ciki yanzu sai kawai a zura ido a ga irin ci gaban da kasar ta Masar zata samu akan hanyarta ta mulkin demokradiyya, ko Ya-Allah zata ci gaba akanta ne ko kuwa zata kauce ta koma tsofon salonta na muzanta wa ‚yan hamayya. Shi dai Mubarak ba da son ransa ne ya share hanyar demokradiyyar ba, matsin lamba ne da ya sha fama da ita daga ketare, musamman ma daga Amurka, ta kai shi ya ba da kai bori ya hau kuma da wuya ya sake mayar da hannun agogo baya.