1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakamakon zaben shugaban kasa zagaye na biyu a Liberia

Zainab A MohammadNovember 10, 2005
https://p.dw.com/p/Bu4L
Hoto: AP

Ratotanni daga kasar Liberia na nuni dacewa an samu fiye da rabin sakamakon kuriu da aka kada a zagaye na biyun zaben shugaban kasa daya gudana a wannan mako.

Kashi 79.5 daga cikin kuriu da aka kada a cibiyoyin zabe dubu 3 da 70 ,na nuni dacewa masaniyar tattalin arzikin nan kuma tsohuwar maaikaciyar bankin duniya Ellen Johnson Sirleaf itace ke jagoranta da yawan kuriu kashi 59.9,ayayinda abokin takaranta kuma fitaccen dan kwallo dake da goyon bayan matasa keda kashi 42.1 daga cikin 100.

Kashi 60.9 daga cikin 100 na yawan wadanda suka cancanci zabe million 1.35 ,inji hukumar zabe na Liberia.

To sai dai tuni Dantakara George Weah ya shigar da kara gaban hukar zaben ,kancewa an tabka magudi a kidayan kuriun da aka kada.

Shugabar hukumar zaben kasar Frances Johnson Morris ta tabbatar da wannan koke da jammiyar CDC ta Mr Weat ta kai gabanta,inda ta kara dacewa hukumarta zatayi iyakar kokarinta na gaggauta bincike cikin wannan koke koke da aka gabatar.

Tace bazat iya cewa komai ba domin bata karanta takardan koken ba,kuma zai kasance abu mawuyaci ta zartar da hukuncin yiwuwar soke zaben,adangane da wannan korafi.

Frances ta fadawa manema labaru a birnin Monrovia cewa zaayi laakari da koke koken ,kafin asan ko zai iya shafar sakamakon wannan zabe.

Tuni dai Weah ya gabatar da wannan koke nasa zuwa kasashen waje ta wajan jamian gani da ido na ketare,domin fatan yin tasiri.

Tun a jiya nedai yayi jawabai ta kafofin yada labaru biyu daya mallaka a kasar ,inda yake kira ga masgoya bayansa dasu gudanar da harkokinsu cikin lumana.

To ayayinda ake dakon sakamako na karshe a dangane da zagaye na biyu tsakanin George Weah da Ellen Johnson,Mdd ta tabbatar dacewa dakarun kiyaye zaman lafiya dake kasar bazasu gaggauta ficewa ,bayan wannan makonba.

A dangane da hakane tace zata tsara shirin gudanarwan sabuwar gwamnatin,tare da janyewan dakarun kiyaye zaman lafiya dubu 15 dake Liberia.

Shugaban ayarin tsaron mdd Chief Allen Doss yace sabon shugaban Libeeria zai fuskanci babban kalubale ,daga sake tsugunar day an gudun hijira zuwa kafa sabuwar rundunar tsaro na matasa..

Doss ya fadawa manema lkabaru cewa wannan babban aiki ne wanda ke bukatar lokaci mai tsawo na cimma hakan.

Yace Mdd zata taimakawa sabuwar gwamnatin Liberian kafa tubali na shugabanci,wadanda suka hadar da samara da tsaro ,da matsalar rashin wutan lantarki da ruwansha,tun bayan kawo karshen yakin basasan kasar shekaru biyu da suka gabata.