1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Al'ummar kasar Burundi na dakon sakamakon zabe.

Lateefa Mustapha Ja'afarJuly 2, 2015

Al'ummar kasar Burundi na can na dakon sakamakon zabukan majalisar dokoki da suka gudanar a Litinin din da ta gabata.

https://p.dw.com/p/1FroZ
Zaben 'yan majalisun dokoki a Burundi
Zaben 'yan majalisun dokoki a BurundiHoto: picture-alliance/AP Photo/G. Ngingo

Jam'iyyun adawar kasar dai sun kauracewa zabukan domin ci gaba da nuna adawarsu da yunkurin shugaban kasar Pierre Nkurunziza na yin tazarce a karo na uku a kan shugabancin kasar. Rahotanni sun tabbatar da cewa sama da mutane 70 ne suka rasa rayukansu tun bayan barkewar gagarumar zanga-zangar adawa da shirin tazarce na Shugaba Nkurunziza a kasar.