1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakamakon zaben yan majalisun dokoki a Masar

November 16, 2005
https://p.dw.com/p/BvKu

A kasar Masar kungiyar yan uwa musulmi, ta bayyana gamsuwa a game da sakamakon da ta samu, a zaben yan majalisun dokoki da a ka yi, a Alkahira da wasu jihohi 7 na kasa.

Kakakin kungiyar ya ce, duk da magudin da gwamnati, ta tabka, sun samu kujeru 34, daga sakamakon da kotu ta bada, ya zuwa yanzu.

A zaben yan majalisa na shekara ta 2000 sun tashi baki daya da kujeru 15.

A lissahin dunan da su ka yi, lokacin yakin neman zabe, yan uwa musuimi na Misra, sun bayana samun a kalla kujeru 50 zuwa 70 daga jimmilar kujerun yan majalisar dokoki 164.

A sahiyar laraba, hukumomin sun bayyana cewa, masu goyan bayan wani dan takarar indipenda, sun kona wani opishi na jam´iya mai rike da ragamar mulki a unguwar Embaba da ke birnin Alkahira.

Jami´an tsaro sun kame 2 daga cikin wanda su ka aikata abin.

Yau ne a ke sa ran samun sakamakon wannan zabe da ya gudana jiya.