1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakataren Majalisar dinkin duniya yayi fatali da bukatar bush game da Iraq

January 18, 2007
https://p.dw.com/p/BuUC

Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki Moon yayi watsi da bukatar da shugaban Amurka George Bush ya mika masa na karin tawagar majalisar a Iraqi.

Ban,ya fadawa manema labari bayan ganawarsa da Bush da shugabanin majalisa a Washington cewa aiyukan majalisar a Iraqi suna da kaida saboda damuwar da take da shi game da harkokin tsaro a kasar ta Iraq.

Kodayake sakataren yace majalisar maida hankali kann sake gina kasar da kuma tabbatar da sauye sauye na demokradiya.