1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakataren tsaron Amirka ya kai ziyara yankin Larabawa

February 18, 2017

Jim Mattis wanda tsohon sojan ruwan Amirka zai gana da shugabannin yankin ko da yake ba a bayyana irin batutuwan da za a mayar da hankali kai ba.

https://p.dw.com/p/2Xq3T
Brüssel NATO Treffen
Sabon sakataren tsaron Amirka Jim MattisHoto: Reuters/F. Lenoir

Sakataren tsaron Amirka Jim Mattis ya isa Hadaddiyar Daular Larabawa a wannan Asabar, a wata ziyarsa ta farko yankin na Larabawa, wata guda da kama aikin.

An dai sa ran zai gana ne da Yerima Mohammad Bin Zayd Al Nahyan na yankin da kuma ministan tsaro Mohammad Al Bawardi.

Tsohon janar na sojan ruwan na Amirka wanda ya fafata yaki a kasashen Iraki da kuma Afghanistan, masanin yankin ne musamman lokacin da yake jagorantar wata runduna.

Ba a dai bayar da cikakkun bayanai kan batutuwan da zai tattauna kansu a ziyarar ba, wanda ke zuwa jim kadan bayan wadansu tarukan da ya halarta a Brussels na Belgium da kuma Munich na Jamus a wannan makon.

Hadaddiyar Daular ta Larabawa dai yanki ne mai muhimmanci a kokarin Amirka na yaki da kungiyar IS da ke kasashen Iraki da kuma Siriya.