1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakatariyar harkokin wajen Amirka na ci-gaba da rangadin kasashen Asiya

October 19, 2006
https://p.dw.com/p/BufL
Sakatariyar harkokin wajen Amirka Condoleezza Rice ta isa babban birnin kasar KTK, Seoul a mataki na biyu na rangadin da take kaiwa kasashe 4 na nahiyar Asiya. Manufar ziyarar tat ta ita ce matsawa KTA lamba bayan gwajin makamin nukiliya da ta yi. Bayan tattaunawar da ta yi da ministan harkokin wajen Japan Taro Aso a Tokyo, Dr. Rice ta yi gargadi KTA da ka da ta kuskura ta sake yin wani gwajin makamin nukiliya. Tana wannan balaguro ne a Japan, KTK, Sin da Rasha da nufin shawo kan kasashen su aiwatar da takunkuman da MDD ta sanyawa gwamnatin Pyongyang. KTA ta bayyana takunkuman da cewa wani yaki ne aka kaddamar a kanta saboda haka zata mayar da martani akan kasashen da suka yi kokarin aiwatar da su.