1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakatariyar Harkokin Wajen Amirka ta isa a birnin Kabul na ƙasar Afghanistan.

June 28, 2006
https://p.dw.com/p/BusR

Sakatariyar harkokin wajen Amirka, Condoleeza Rice, ta isa a birnin Kabul na ƙasar Afghanistan, inda za ta yi shawarwari da shugaba Hamid Karzai. Rice ta taso ne daga birnin Islamabad na ƙasar Pakistan, bayan ganawarta da shugaba Pervez Musharraf. Kafin ta baro Pakistan ɗin dai, Rice da shugaba Musharraf sun ba da sanarwar cewa, Pakistan za ta girke dakaru dubu 10 a kan iyakarta da Afghanistan, don hana ’yan ƙungiyar Taliban kai kawo a yankin. Ita dai Rice, ta kuma shawarci Pakistan da Afghanistan da su daina hamayya da juna, su fi ba da himma wajen haɗa kai don yaƙan ’yan tawaye a kan iyakarsu. Ziyarar tata dai ta zo ne a daidai lokacin da mayaƙan ƙungiyar ’yan Taliban ɗin ke ta iza wuta a gwagwarmayar da suke yi da dakarun ƙetare a Afghanistan.