1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

200810 DDR Volkskammerbeschluss

August 23, 2010

Shekaru 20 kenan da aka sake samun haɗin kan Jamus.

https://p.dw.com/p/OuLj
Gregor GysiHoto: picture alliance/dpa

Daren 23 ga watan Agustan shekarar 1990 na zaman dare mai tarin muhimmaci a tarihin Tarayyar Jamus, bayan yaƙin duniya na biyu, saboda kasancewarsa daren da a cikinsa mahukunta a gabashin birnin Berlin suka tsai da shawarar haɗe ɓangarensu wato Jamus ta Gabas da Jamus ta Yamma.Halima Balaraba Abbas na da karin bayani......

"Ɗazu-ɗazun nan ne majalisar dokoki ta tsai da shawarar haɗe Jamus ta Gabas da Jamus ta Yammaci ba da wani ka ce na ce ba."

Gregor Gysi kenan shugaban ɓangaren jam'iyyar PDS, wadda ta maye gurbin jam'iyyar komisanci ta SED, a ranar 23 ga watan Agustan shekarar 1990, ke ba da sanarwar haɗewar Jamus ta Gabas da Jamus ta Yamma somi da ranar 3 ga watan Oktoban shekarar 1990.

Wasu yan kwanaki gabanin haka babu wani zama da aka yi ba tare da 'yan majalisar sun buƙaci gaggauta haɗe Jamus ta Gabas da Jamus ta Yamma ba. Lothar de Maiziere shi ne fraministan Jamus ta Gabas a wancan lokaci. Ya yi tsoƙaci game da buƙatar al'uma ta haɗe Jamus ta Gabas da Jamus ta Yamma a cikin gaggawa da kuma dalilin naɗa sabuwar majalisar dokoki a watan Maris na shekarar 1990: Ya ce "Bayan zaman da muka yi a ranar 22 ga watan Agusta da rana sai da na buƙaci a yi wani zama na musannan a wannan ranar ɗin domin duba lokacin da ya dace a samu haɗin kan Jamusawa."

20.08.2010 Dw-TV Typisch Deutsch Lothar de Maiziere
Lothar de MaiziereHoto: DW-TV

To sai dai kuma an samu wasu 'yan majalisa da suka nuna rashin amincewa da gaggauta haɗe ɓangarorin biyu saboda tsoron da suka yi cewa mai yiwuwa ne a sadakau da buƙatun Jamus ta Gabas. Wolgang Ullman wanda ya riƙe muƙamin ministan da ba shi da wata ma'aikata a ƙarƙashinsa, na ɗaya daga cikin masu wannan ra'ayi, wanda ya buƙaci a ƙirƙirar da wani sabon kundin tsarin mulki na Jamus ta Gabas domin kare buƙatun Jamus ta Gabas bayan shiga sabon babi. A ranar 22 ga watan Agustan shekarar 1990 ne dai Lothar de Maiziere ya yi ƙoƙarin katse masa wannan hanzari. Maiziere ya ce: "sai da Mataimakin Shugaba, Wolfgang Ullmann ya zo wurina ya gaya mani cewa zai je gun babban lauyan Jamus ta Gabas domin shigar da ƙara akaina bisa lafin cin amana. Daga nan ne kuma aka yi zaman komitin shugabanni a ƙarƙashin jagorancin Rheinhard Höpper, shugaban jam'iyyar SPD wanda ya tambaye ni ko shin na yi amanna da wannan ƙara? Sai na ba shi amsa na ce ba zan shigar da wanan buƙata a majalisa ba, alabashin daga baya in nemi janyeta."

Mitbegründer von Demokratie jetzt Konrad Weiss und Wolfgang Ullmann
Wolfgang Ullmann, ta dama, tare da wasu manyan jami'an Jamus ta Gabas a ranar 22.01.1990.Hoto: picture-alliance/ ZB

A dai zama na musamman da aka yi a baya; ba a koma yin magana game da ko shin Jamus ta Gabas ta yi bayani game da ayar kundin tsarin mulkin Jamus ta yamma akan haɗewar ɓangarroin biyu ba. Sai da wasu 'yan majalisa suka nuna rashin amincewa da shawarar fraministan ta gudanar da zaɓe game da wannan batu a ranar 14 ga watan Oktoba. A baya ga 'yan jam'iyyar PDS babu wanda ya so ganin ranar 7 ga watan Oktoba, a matsayin ranar bukin cika shekaru 41 na kafuwar Jamus ta Gabas.

An dai gama aiki tare da samun yardar al'uma game da sake haɗewar Jamus ta Gabas da Jamus ta Yamma, shekaru 28 bayan gina kantangar Berlin. A wancan lokaci gwamnatin Jamus ta Yamma da ke da mazauninta a birnin Bonn ta yi ɗari -ɗari wajen tattauna wannan tafarki, wanda a yanzu a lokaci-lokaci ake masa kallon wani abu na daban.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas

Edita . Ahmad Tijani Lawal