1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sake haduwa da dangi bayan rabuwa

February 8, 2017

Gidan radiyon kasa da kasa na Dandal Kura Internationalda ke watsa shirye-shiryensa a Maiduguri fadar gwamnatin jihar Borno, ya bullo da wani shiri na hada iyalan da suka rabu sakamakon Boko Haram.

https://p.dw.com/p/2XBzy
Usman da mahaifiyarsa sun sake haduwa bayan harin Boko Haram ya raba su
Usman da mahaifiyarsa sun sake haduwa bayan harin Boko Haram ya raba suHoto: Reuters/TRF/K. Guilbert

Dubban iyalai ne dai suka tarwatse saboda hare-haren da kungiyar Boko Haram ke kai wa musamman a yankin Arewa maso Gabashin Tarayyar Najeriya, kana wannan shiri dai ya haifar da gagarumar nasara wajen hada iyalai da suka shafe shekaru ba su san inda 'yan uwan su suke ba. Alhaji Faruk Dalhatu da ke zaman manajan darakta na wannan gidan radiyon ya nunar da cewa sun yi shawarar bullo da shirin ne da nufin tallafa wa rayuwar iyalan da ke cikin halin zullumi da fargaba na rashin sanin inda danginsu suke wadanda hare-haren na Boko Haram ya tarwatsa a ciki da wajen jihar ta Borno. Ya ce wurare da dama kafa ba ta iya zuwa amma gidan radiyo ka iya kai wa ta yadda dangin wadanda suka bace ka iya jin inda 'yan uwansu suke.

A jawabinsa yayin wata ziyarar aiki da ya kai gidajen radiyon yankin Arewa maso Gabashin Najeriya da nufin kara karfafa huldar dangantakatr da ke tsakaninsu da tashar DW, shugaban sashen Hausa na tashar radiyon DW din Malam Thomas Mösch ya nuna matukar farin cikinsa da jin dadi, ganin yadda tashar ta Dandal Kura International ke kokarin hada iyalan da suka rabu na tsahon shekaru. Yacilla Bukar ita ce ke jagorantar wannan shiri da ake wa lakabi da "Ina Kake?" ta ce tana matukar jin dadin shirinta kasancewa tana hada mutane da 'yan uwansu kuma suna yi mata addu'a. Suma wasu da suka samu nasarar haduwa da 'yan uwansu ta wannan shiri na Dandal Kura International sun nuna farin cikinsu, yayin da wasu kuma suka gabatar da kansu da nufin a cikito musu nasu dangin.