1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakin fursinonin Koriya ta Kudu a Afghanistan

August 30, 2007

Kasar Koriya ta Kudu ta ba da kai bori ya hau domin ganin an saki 'yan kasar da Kungiyar taliban ke garkuwa da su

https://p.dw.com/p/Btue
Fursinonin Koriya ta Kudu a hannun Red Cross
Fursinonin Koriya ta Kudu a hannun Red CrossHoto: AP

A hakika dukkan dangin fursinonin na da cikakken ‚yancin nuna doki da murna a game da sake saduwa da ‚yan uwansu, amma fa a daya bangaren wannan ci gaba ka iya haifar da wani mummunan sakamako. Domin kuwa wannan shi ne karo na farko da wata gwamnati ta amince ta shiga tattaunawa kai tsaye kuma a hukumance tare da ‚yan ta’adda tana mai fatali da ka’idar da aka saba amfani da ita a irin wannan hali a zamanin baya. Bugu da kari kuma ko da yake kasar Koriya ta Kudu tun da dadewa ta tsayar da shawarar janye sojojinta daga kasar Afghanistan, lamarin da a yanzu kungiyar Taliban ke bayyana farin cikinta da shi, amma fadar mulki a Seoul ta ba wa masu garukuwa da fursinonin wata dam ata yada farfagandarsu a kafofin yada labarai. A baya ga haka a sakamakon wannan mataki da ta dauka a yanzu babu wata kungiyar taimako ta kirista da zata yarda ta tura ma’aikatanta zuwa kasar domin gudun ka da su wayi gari a matsayin karnukan farauta ga ‚yan Taliban. Kazalika wannan ba da kai bori ya hau da gwamnatin Koriya ta Kudu tayi tamkar lasin ne ga kungiyoyi na ‚yan ta kife domin su rika azabtar da fursinonin da suke garkuwa da su tun da hakan ne zai kai su ga samun biyan bukata. Tilas a yi fagabar wannan ci gaba bam a a Afghanistan kadai ba har da kasashe irin su Iraki inda garkuwa da fursinoni ya zama ruwan dare tare da neman janyewar sojojin ketare daga cikinta. Jamus ita ce kasa ta farko da zata fara jin radadin wannan mataki saboda har yau akwai dan kasar dake tsare a hannun wasu masu neman amfani da shi domin ci da ceto, kuma mai yiwuwa a yanzun su kara tsaurara sharuddansu game da sakinsa. Ko da yake ba wanda ya san yadda al’amura zasu kaya da kasar Koriya ta Kudu ta ci gaba da hakuri da juriya, amma a zamanin baya an ga yadda aka kawo karshen ire-iren wannan matsala ta garkuwa da farar fula ba tare da an zub da jini ba. Amma tun daga yau alhamis al’amura sun canza sun dauki wani sabon fasali mai sarkakiyar gaske bam a ga gwamnatocin kasashe ba har da jami’an taimako na ketare dake ba da gudummawa a kokarin sake gina kasar Afghanistan da yaki yayi kaca-kaca da ita.