1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakin Jamusawa a Iraqi

May 2, 2006
https://p.dw.com/p/Buzp

Maáikatar harkokin wajen Jamus ta sanar da cewa an sako Jamusawa biyu da yan takife suka yi garkuwa da su a Iraqi. Ministan harkokin wajen Jamus Frank Walter Steinmeier wanda yake ziyarar rangadi a latin Amurka yace har ma ya yi magana da mutanen biyu ta wayar tarho wadanda ya baiyana da cewa suna cikin koshin lafiya. Jamusawan biyu, Thomas Nitzchke mai shekaru 32 da haihuwa da Rene Bräunlich dan shekaru 28 wadanda dukkanin su injiniyoyi ne daga jíhar Leipzig, suna aiki ne da wani kamfanin Jamus a arewacin Iraqi kafin yan bindiga dadi su sace su, a yankin masanaántu na garin Baiji a ranar 24 ga watan Janairu. Wadanda suka yi garkuwa da su, da kuma suka baiyana kan su da sunan kungiyar Ansar al-Tawheed wal Sunna sun yi barazanar kashe jamusawan biyu idan aka yi burus da bukatun su na sakin dukkanin fursunonin da Amurka ke tsare da su a Iraqi.