1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakin Susanne Osthoff

December 19, 2005

A yammacin jiya lahadi ne aka samu rahoton sakin Susanne Osthoff da aka yi garkuwa da ita a Iraki

https://p.dw.com/p/Bu3H
Susanne Osthoff
Susanne OsthoffHoto: AP

A yanzun dai an kawo karshen dardar da aka rika yi dangane da makomar Susanne Osthoff. To sai dai kuma har yanzu babu wani bayani dalla-dalla da aka samu dangane da masu alhakin garkuwa da ita da kuma ainifin sakinta da aka yi. Mai yiwuwa za a ci gaba da boye dukkan wadannan bayanai domin kare makomar masu alhakin garkuwa da ita, wadanda bayan makonni uku suka canza shawara akan manufa. Muhimmin abu, kuma mafi alheri shi ne ka da a mayar da nahkali wajen bin diddigin masu alhakin wannan ta’asa ko binciken dalilansu, sa’o’i kadan bayan sakinta. Wasu bayanai dai sun ce wai ba an yi garkuwa da Susanne Osthoff ne a saboda dalilai na kudi ko na siyasa ba, sun tsare ta ne saboda zaton da suka yi na kasancewarta ‚yar leken asiri. Kome ne ne dai dalilin nasu, ba abu ne da ya cancanta ba da a yi garkuwa da farar fula tare da barazana game da makomar rayuwarsu. Dukkan wadanda lamarin ya shafa dai sun Hamdallah a game da sakin malamar tone-tonen kayan tarihin. Wannan mataki na garkuwa da ita da aka dauka a kasar Iraki ya wayar da jama’a cewar Jamusawa daidai da Faransawa suna fuskantar barazana a game da makomar rayuwarsu a kasar Iraki duk da kasancewar ba su da hannu a matakin gabatar da yaki kann wannan kasa. Ita kanta Faransa ta sha fuskantar matsalar garuwa da ‚ya’yanta, abin da ya hada har da ‚yan jarida a kasar ta Iraki. Kazalika hakan na mai yin nuni ne da cewar ba wanda ya tsira daga ta’asar ‚yan ta’adda saboda matakinsu shi ne kamar haribi ne na kann mai uwa da wabi. Muhimmin abin da suka sa gaba shi ne ta da zaune tsaye da hana wa jama’a kwanciyar hankali wajen gudanar da harkokin rayuwarsu ta yau da kullum. Ita dai Susanne Osthoff daya ce daga ‚yan kasashen waje ‚yan kalilan da suka yi koburus da ire-iren wannan barazana ta garkuwa da farar hula a kasar ta Iraki a fafutukarsu ta ba da gudummawa iya gwargwado wajen sake farfado da al’amuran kasar da yaki yayi kaca-kaca da ita. Domin kuwa a baya ga sojoji, galibi zaka tarar da akasarin ‚yan kasashen ketare dake tsunduma zuwa kasar barayin na-tsinta ne, wadanda ke amfani da mawuyacin halin da jama’a ke ciki domin ci da guminsu. Abin takaici a nan dai shi ne kasancewar, a nan Jamus, bisa sabanin Faransa da Italiya, ba wanda ya fito fili ya jinjina wa Susanne Osthoff ko ya shiga zanga-zangar neman da a sake ta, duk kuwa da hakikancewar da aka yi cewar taimakon jinkai shi ne ainifin makasudin ci gaba da zamanta a kasar Iraki. Ga alamu harkokin kasuwancin bikin kirismeti shi ne a’ala ga jama’a akan maganar zanga-zangar neman sakin wata da ake garkuwa da ita a Iraki. Amma fa wajibi ne a fahimci cewar Allah waddai da wani mataki yaki ba shi ne kadai a’ala ba, kazalika wajibi ne a tashi tsaye a taimaka wa mutanen da kaddara ta rutsa da su. Wannan shi ne ainifin sakon dake tattare da garkuwar da aka yi da Susanne Osthoff da kuma sakinta daga bisani.