1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakon sabuwar shekara daga shugabar gwamnatin Jamus

December 31, 2007
https://p.dw.com/p/CiZo

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce ƙasar Jamus ta samu ci gaba fiye da lokacin da jam’iyun haɗaka suka karbi ragamar mulkin ƙasar a 2005. cikin saƙonta na sabuwar shekara shugabar ta Jamus tace a karon farko tun sake haɗewar ƙasar Jamus a 1990, ƙasar ta kusa cimma kasafin kuɗi da ya daidaita yayinda kuma ta inganta fannonin bincike da ilmi. Merkel ta ce ɗaya daga cikin muhimman ababen da gwamnatinta ta samu nasara a kai shine rage yawan marasa aikin yi masu yawan gaske. A hannu guda kuma Merkel ta yi gargaɗi game da wasu batutuwa na tattalin arziki da tace zasu iya zama haɗari ga nasarar da Jamus ta samu a fannin tattalin arzikinta. Ta kuma sha alwashin cewa ƙasar ta Jamus mafi ci gaban tattalin arziki a nahiyar Turai zata ci gaba da ƙoƙarinta na kawadda rashin aikin yi baki daya a ƙasar.