1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakonnin taaziyya zuwa Amurka adangane da mutuwan tsohon shugaba Ford

December 27, 2006
https://p.dw.com/p/BuWF

Gwamnatocin kasashen duniya nacigaba da bayyana marigayi tsohon shugaban Amurka Gerald Ford,da kasancewa fitaccen shugaba,daya jagoranci kasassa alokacin da take cikin mawuyacin hali.Shugaban jamus Horst köhler,a wasikar daya aike wa shugaba Bush,ya bayyana marigayin da kasancewa wanda ya taka rawar gani wajen kafa kungiyar kasashe masu cigaban masanaantu guda 8.Bugu da kari shugab Pervez Musharraf na pakistan da takwaransa na Croatia Stipe Mesic,sun bayyana Ford da kasancewa mutumin da zai kasance cikin tarihi wajen fafutukar kwace hakkin biladama.Shugaba George W Bush a nashi bangaren ya bayyana juyayain amurkawa adangane da mutuwan tsohon shugaba Ford.Mai shekaru 93 da haihuwa,Gerald Ford wanda ya shugabanci Amurka daga 1974 zuwa 1976,ya mutu ne yau da safiya a gidansa dake Califonia.