1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Salon mulkin Togo da Yuganda sun mamaye jaridun Jamus

Zainab Mohammed Abubakar
September 15, 2017

Jam'iyyun adawar kasar 14 suka kira wani gangamin, wanda a baya ga fadar gwamnati ta Lome, ya bazu zuwa wasu garuruwan kasar ta Togo. Tuni dai gwamnati ta bada umurnin cafke 'yan adawar.

https://p.dw.com/p/2k4XL
Faure Gnassingbe, Präsident Togo
Hoto: AFP/Getty Images/I. Sanogo

Jaridar Neue Zürcher Zeitung kan rikicin siyasar da ya kunno kai a kasar Togo da ke Yammacin Afirka ta maida hankali a kansa. labarin mai taken" Kusan shekaru 50 iyali daya ne ke mulki a Togo". Yanzu gwamnati na fuskantar barazanar sauyin alkibla daga boren al'umma".

Jaridar ta cigaba da cewar tun a tsakiyar makon da ya gabata ne dai, wannan 'yar karamar kasa ta Afirka ta fada rigingimun zanga-zangar adawa da gwamnati. Dubban daruruwan 'yan kasar ne suka bazama kan titi, su na kira ga Shugaba Faure Gnassingbe da ya yi murabus daga kujerar mulki.

Proteste in Togo gegen Gnassingbe ARCHIV
Masu adawa da gwamnatin kasar TogoHoto: picture alliance/AA/ Alphonse Ken Logo

Jam'iyyun adawar kasar 14 da suka kira wannan gangamin, wanda a yanzu baya ga fadar gwamnati ta Lome, ya bazu zuwa wasu garuruwan kasar ta Togo. Tuni dai gwamnati ta bada umurnin cafke 'yan adawan, a lokaci guda kuma ta yi alkawarin gyaran kundin tsarin mulki ta yadda za'a takaita wa'adin mulkin ko wane shugaban kasa zuwa guda biyu. Sai dai wannan sauyi ba zai shafi wa'adin mulkin da suka gabata ba, batu da ke nufin shugaba Gnassingbe da ke mulki tun daga shekara ta 2005, zai fara nashi wa'adin ne daga yanzu, bisa ga sabuwar dokar. Sai dai tuni 'yan adawa suka sa kafa suka shure wannan shirin doka, tare da cigaba da gudanar da zanga zanga a fadin kasar ta Togo

Ita kuwa jaridar Die Tageszeitung sharhi ta rubuta game da halin da ake ciki a dangane da yiwuwar gyaran kundin tsarin mulki na rage adadin shekarun yin takarar shugaban kasa, bisa ga tanadin na yanzu dai wanda ya haura shekaru 75 ba zai iya shugabancin kasar ba.

Janet Museveni  Yoweri Museveni
Janet Museveni da Yoweri MuseveniHoto: picture alliance/dpa/D.Kurokawa

Shugaba Yoweri Museveni na Yuganda mai shekaru 71 da haihuwa ya kasance akan mulki tun daga shekara ta 1986. Kuma zai iya tsayawa takara ne a zaben shugaban kasa na gaba a shekara ta 2021 kadai, idan an janye wannan doka ta hanyar gyaran kundin tsarin mulki.

'Yan majalisa 293 daga cikin 426 ne dai suka amince da wannan sauyi a zaman da aka yi a hukumance a ranar Alhamis, batu da  ke zama kamar an tsara shi ne.

Daga batun siyasa a Togo da Yuganda sai kuma yaki da zazzabin cizon sauro na Maleriya, jaridar Der Tagesspiegel ta ce bisa dukkan alamu dai an doshi samun mafita dangane da wannan cuta da ta samu gindin zama a kasashen nahiyar Afirka.

Mosquito
Hoto: Alan R. Walker / CC BY-SA 3.0

Wata cibiyar bincike a California ta dukafa ka'in da nain wajen binciken hanyoyin da za'a shawo kan wannan matsala da ta jima ta na hallaka rayukan al'umma a nahiyar Afirka. A Tanzaniya dai masana kimiya sun fara amfani da shanu da waki wajen gwajin magungunan, kuma ya zuwa yanzu sun yaba da nasarar da aka samu, kamar yadda jaridun yankin gabashin Afirkan suka wallafa.

A shekara ta 2015, MDD ta kiyasta cewar wajen mutane miliyan 212 suka kamu da cutar ta maleriya a fadin duniya.