1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Samakon zaben Faransa

April 23, 2007

Sarkozy da Royal su ne zasu shiga zagaye na biyu a zaben neman zama shugaban kasar Faransa a 6 ga watan mayu

https://p.dw.com/p/Btvi
Zaben kasar Faransa
Zaben kasar FaransaHoto: AP

Sakamakon da aka bayar a hukumance, wanda bai hada da kuri’u dubu dari takwad da ashirin na ‘yan kasar Faransa dake zama a ketare ba, ya bai wa Sarkozy kashi 31 sannan ita kuma Segolene Royal kashi 25%. Dangane da Francois Bayrou mai sassaucin ra’ayi da kuma Jean Marie Le Pen mai kyamar baki ba su kai labari ba, inda Bayrou ya tashi da kashi 18 shi kuma Le Pen kashi 11 cikin dari. Gaba daya kimanin kashi 65% na mutane miliyan 44 da rara dake da ikon kada kuri’a ne suka shiga zaben na jiya lahadi. Wannan adadi kuwa shi ne mafi girma da aka samu a cikin shekaru 40 da suka wuce. Nan da makonni biyu za a koma zagaye na biyu na zaben tsakanin Sarkozy da Royal. A hakika kuwa wannan sakamkon bai zo a ba zata ba. Su dai Faransawa, fatansu shi ne a fuskanci wata takamamiyar mahawara ta siyasa tsakanin ‘yan takarar guda biyu kafin wa’adin zaben zagaye na biyu a ranar 6 ga watan mayu mai kamawa. Ita ma Jamus tana fatan ganin hakan ya faru saboda ta san takamaimiyar alkiblar da kowane daga cikin ‘yan takarar ya fuskanta dangane da manufofin Turai da kuma dangantakar Jamus da Faransa. Domin kuwa a yake-yakensu na neman zabe, a wannan karon ‘yan takarar sun gabatar da jerin batutuwa daban-daban, bisa sabanin yadda lamarin ya kasance shekaru biyar da suka wuce, inda aka fi mayar da hankali akan maganar tsaron lafiyar jama’a a cikin gida. Misali Nicolas Sarkozy, a yake-yakensa na neman zabe ya fi bayar da la’akari ne ga matakan da zasu taimaka masa ya kwace wa Jean-Marie Le Pen magoya baya, inda ya rika yayata maganar korar illahirin bakin haure daga Faransa da kuma kafa wata ma’aikata ta kaka-gida. Ana dai zarginsa da daukar matakai na ba sani ba sabo don kawar da masu adawa da manufofinsa kai har ma da muzanta wa ‘yan jarida. Ita kuwa Segolene Royal ta mayar da hankalinta ne akan abin da ta kira wata sabuwar manufa ta demokradiyya dake bai wa jama’a cikakkiyar damar shiga a dama da su kai tsaye a al’amura na yau da kullum. A dai ranar 6 ga watan mayu za a sake komawa zagaye na biyu don fid da gwani tsakanin ‘yan takarar guda biyu kuma wajibi ne su sauya take-taken su dangane da matsaloli iri daban-daban dake addabar kasar Faransar a halin yanzu haka.