1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Samar da makamashi a Afirka

June 16, 2010

Akwai Kalubalen samar da makamashi dake gaban kasashen Afirka kudu da sahara, musamman yin anfani da fasahar zamani.

https://p.dw.com/p/NsGX
makamcin hasken ranaHoto: DW-TV

A dai dai lokacinda ƙasashen da suka ci gaba, basa rayuwarsu takansace ba ta yiwuwa in ba tare da wutar lantarki ba, to amma har yanzu a ƙasashen masu ta sawo kamar na Afirka kudu da sahara, ana fama da ɗimbin matsalolin rashin wutar lantarki, inda a birane wutar bata wodatar ba, a karkara kuma kusan babu ita. Usman Shehu Usman ya rubuta mana rohoto.

A ƙasashen na kudu da sahara dai aksari an dogara kan itatuwa wajen girki, abinda kuma yake haddasa kwararowar hamada, da sauyin yanayi. Sare dajin da ake yi ya rubbayan ayyukan samar da wuta ta hasken rana da yanyar iska dake kaɗawa, waɗan da da anyi amfani da su zai samar wa ƙasashen kuɗin shiga da kyautata tattalin arzikinsu. Amma idan aka duba yadda wayar salula ta yi saurin yaɗuwa to ana iya cewa komai zai iya kasancewa idan ana son yinsa da gaske. Ibrahim Togola shine daraktan wata ƙungiya mai zaman kanta wanda take kula da kare mahalli dake a yammacin Afirka.

"Ka ɗauki misalin ƙasar Mali, muna da layin tarho ƙasa da dubu ɗari shida. Amma ga wayar Salula, yanzu muna da masu amfani da ita kimanin miliyan uku a ƙasa da shekaru goma. A ganina idan muka yi la'akari da wannan, to muna iya samar da wutar lantarki ta hasken rana, ko kuma yin amfani da sharar da muke zubarwa, ko ta hanyar amfani da iska dake kaɗawa, don samar da wutar lantarki. Bama buƙata cewa sai mun samar dukkan ƙasa wuta, muna iya amfani da ƙwararun mutane da muke da su, don samar da wani abu mai amfani fiye da yadda aka zata. Kuma wannan zai sa mu manta da dogaro da mai ko iskar gas"

Waɗannan kalamai da shawarin da Togola yake zayyanawa abune da man'yan kamfanoni dake samar da wutar lantaki, ko kuma masu haƙar mai a duniya, basa san ji, domin idan hakan ta faru, su kuwa basu da kasuwa. To amma sai dai ƙungiyoyin bada agaji kamar su Bankin duniya da hukumar raya ƙasace ta Majalisar Ɗinkin Duniya suna bayyana cewa, idan muka fara ɗaukar waɗannan matakai shine mafi alheri ga ƙasace masu tasowa.

Sadai mutane irinsu Ibrahim Togola na ganain cewa ana iya ƙarfafa samar da wutar lantarki na ƙasa, inda a gefe guda, ana iya samarwa yankunan karkara a kafa musu ƙanan kamfanoni kamar na sauya sharar da ake zubarwa, ko kuma na iskar dake kaɗawa, dama hasken rana don samar musu da wutar lantarki. A yanzu haka haɗin gyiwar kamfanin samar da wuta ta hasken rana dake Jamus mai suna Solar World da ƙungiyar Mali Folkencenter wanda Togola yake jagoranta sun samar da wutar lantarki a wani asibiti dake ƙasar ta Mali, kuma yana aiki yadda yakamata. Claudia Hanisch itace kakakiyar ƙungiyar ta Solar World. inda tacke cewa

Muna wani tsari na samar da taƙaitaccen wutan lantarki, wanda zai iya isan ƙananan ƙauyuka. Wato ma'ana zaka iya kafa cibiyar wutan a tsakar ƙauyen, wannan yana nufin ko wane ƙauye na iya kafa wutar lantarki na kansa"

Abinda aka rasa dai bawai fasahar ba, a'a sai dai kwai babu bankuna a karkara dake bada bashi, kamar yadda Irahim Togola ya bayyana.

"Ƙanan bankuna waɗan da za su mai da hankali kan samar da wuta ta fannoni na zamani, ta yadda al'ummomi dake ƙauye za su iya ayyukan taimakon juna, amma kuma muna buƙatar waɗan da za su bada bashi domin tayar da fannin noma"

Kamar yadda ta faru a ƙasar Jamus inda ake baiwa masu inganta irin waɗannan sana'o'i bashi, to ta hakane kawai su ma ƙasashen Afirka za su samu haɓaka, kamar yadda Ibrahim Togola wanda ya kafa kamfaninsa shekaru 12 da suka gabata, amma yanzu yana da ma'aikata kimanin 42.

Mawallafa: Usman Shehu Usman da Richard Fuchs

Edita: Ahmadu Tijjani Lawal