1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Samar da zaman lafiya a Yankin gabas ta tsakiya

Zainab MohammedDecember 5, 2007

Irin rawa da Syria zata taka

https://p.dw.com/p/CXVD
Shugaba Bashar Assad,na Syria da Ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter SteinmeierHoto: AP

Gwamnatin Amurka dai ta jima tana yiwa Syria kallon shaiɗaniyar kasa,adangane da dangantaka na kut da kut da take dashi da Iran,tare da zargin ta da marawa ƙungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi kamar na Hamas dake yankin Palasɗinawa da Hizobollahi na Lebanon baya,sai dai wannan tunani na Amurka ya samu sauyi bayan data amince da ɗaukar nauyin fafutkan samar da zaman lafiya a yankin na Gabas ta tsakiya.

Amurkan dai a yanzu haka ta saka ƙasar ta Syria cikin kokarin da akeyi na samar da zaman lafiya a rikivcin da yankin gabas ta tsakiya ke fama dasu.A yanzu haka kuma Gwamnatin ƙasar Faransa ta gayyaci Syrian zuwa taron ƙasa da ƙasa da za a gudanar a Paris ,domin tallafawa yankin Palasdinawa a tsakiyar wannan wata na Disamba da muke ciki.

Syria dai nada muhimmiyar rawa da take takawa a dukkannin a,amura na yankin gabas ta tsakiya musamman a ɓangarorin dake adaw da juna a yankin Palasɗinawa,kamar yadda take da tasiri a ƙasar Libanon,inda ake saran ‘yan majalisa zasu taɓi sabon shugaban ƙasa.idan Allah maɗaaukakin Sarki yakai mu.

Kawo zuwa yau dai ana cigaba da darajawa kalaman nan da tsohon ministan harkokin wajen Amurka Henry Kissinger ya taɓa yi dangane da yankin gabas ta tsakiya,na cewar duk wani tashin hankali daya ritsa da yankin akwai hannun Masar aciki,ayayin da a hannu ɗaya kuwa,baza a iya samar da zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya ba tare da ƙasar Syria ba.Koda yake wasu na ganin cewar wannan kalaman ba daidai suke ba ,ganin yadda dakarun Izraela ke cigaba da cin karensu babu babbaka ,wanda ya haɗar da yakin da suka gwabza da ‘yan Hizobollahi ,da ƙungiyoyin masu tsattsauran ra ayi na addinin Islama,dake yankin Palasdinawa.

Sai a ɓan garen Syria,Diplomasiyyan Jamus ya taka rawa musamman wajen sauya alkiblar kasashe kamar Amurka a dangane da lamuranta.Zaa iya ganin matakin farko na wannan sauyin Alkibla a gayyatar Syria da Amurkan tayi zuwa taron samar da zaman lafiya a birnin Annapolis.Hakan na nuni dacewar a yanzu Amurkan tac ire Syria daga jerin shaiɗanun kasashe data bayyana abaya.

Tun a bara bayan rangadin aikin daya kai birnin Damaskus nedai,Ministan kula da harkokin waje na tarayyar Jamus Frank Walter Steinmeier ya hakakance cewar ,ayanzu Syria ba ta da hannu a rigingimun yankin da ake zarginta dasu.Inda Steinmeier ya yabawa manufofin Shugaba Basha al-Assad na fatan ganin cewar a gano bakin zaren warware rikicin yankin gabas ta tsakiya.”Na samu tabbacin cewar Syria tana da manufofi data sanya a gaba waɗanda take fan cimmawa.Shugaban ya shaidar min dacewar ƙasarsa tana yin garon bawul wa harkokinta na kasuwanci da siyasa tare,domin suna neman masu zuba jari ,tare da samara matasa wuraren aiki”

Shugaba Bashar al-Assad dai yana sane dacewar cimma waɗannan manufofi da gwamnatinsa ta sanya gaba na bukatar tallafi hannaye daga ketare.Sai kowane haɗin kai ake buƙata yana da matukar wahalar samu.Adangane da haka ne ya fito fili ya bayyana manufofin sa.Ba fatan sa bane a koma shekarar 1967 lokacin Izraela ta mamayar tsaunukan kasarsa na Golan ba.Kazalika yayi alkawarin taimakawa bincike da akeyi dangane da kisan gilla da akayi wa tsohon premiern Libanon Rafik al-Hariri.

Syria dai dai ta bayyana kyawawan manufofin ta adangane da halartan taron samar da zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya da aka gudanar a birnin Annapolis ɗin Amurka,wanda kuma ko kaɗan tace bazai shafi dangantakarsu da ƙasar Iran ,wadda ta nuna rashin jin daɗin ta ba.Manazarta dai na cigaba da jaddada cewar ingantuwan dangantaka tsakanin Syrian da sauran ƙasashen yammaci da kuma Amurka,zai taimaka wajen cimma manufofin samun zaman lafiya da aka sanya a gaba dangane da yankin na gabas ta tsakiya,rikicin daya ƙi ci yaƙi cinyewa.