1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sanarwar gwamnatin Jamus akan taron G8

May 24, 2007

A yau alhamis shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ba da sanarwar manufofin gwamnatinta dangane da taron G8

https://p.dw.com/p/BtvW
Angela Merkel
Angela MerkelHoto: AP

Shugabar gwamnati Angela Merkel ta ce bai wa manufar nan ta kusantar sassan duniya a manufofi na kasuwanci da zamantakewa wata suffa ta kasa da kasa da ta dace da ita shi ne muhimmin abin da gamayyar kasashen G8 ta sa gaba. A sakamakon haka aka bai wa taron kolin na Heiligendamm take:”Bunkasar tattalin arziki da sanin ya kamata.” Hakan na ma’ana ne cewar gaggan kasashe takwas da suka fi ci gaban masana’antu a duniya zasu kara ba da la’akari da irin alhakin da ya rataya a wuyansu a game da makomar damngantaku na kasa da kasa. To sai dai kuma ba zata yiwu a samu ci gaba ba face tare da kasashe masu matsakaicin ci gaban masana’antu kamarsu China da Indiya da Brazil. A sakamakon haka aka gayyace su domin halartar taron kolin na Heiligendamm. Merkel tayi bayani a game da wasu manufofi bakwai da taron kolin zai mayar da hankalinsu, kuma ta bakwai daga cikin wadannan manufofi ita ce ta dangantaka da Afurka. Merkel ta kara da cewar:

“A bangare guda akwai maganar muhimman alkawurrukan da muka yi a shekarun baya-bayan nan a game da bunkasa yawan taimakon raya kasa da muke bayarwa. Zamu cika wadannan alkawururruka, kamar yadda nike bayyana muku a fili. Amma a daya bangaren muna fatan ganin kawayenmu a nahiyar Afurka sun ci gaba da daukar nagartattun matakai na garambawul ga manufofinsu.”

Daya maganar kuma ta shafi manufar kare makomar yanayi ne, sai kuma sassaucin huldodin ciniki tsakanin kasashe, wadda shugaban jam’iyyar hamayya ta FDP Guido Westerwelle ya bayyana tababarsa game da ita inda yake cewar:

“Shugabar gwamnati kina da gaskiya idan kin yi batu a game da cewar wajibi ne su ma sauran kasashe su bude kofofin kasuwanninsu ga kayayyaki daga kasashen Turai, amma a lokaci guda wajibi ne mu yi adalci wajen nuna cewar ainifin wannan maganar ta fi shafar kasashen Turai idan an ba da la’akari da kayan amfanin noma. Wajibi ne a kamanta adalci wajen ba wa sauran kasashe cikakkiyar dama ta cinikin amfanin da suke nomawa a nahiyar Turai.”

Shi kuwa kakakin jam’iyyar hamayya ta the Greens Fritz Kuhn bayyana tababarsa yayi a game da cewar a hakika taron na Heiligendamm zai haifar da wani sakamako na a zo a gani. Ya ce ko da yake sanarwar gwamnatin ta kunshe nagartattun manufofi, amma fa babu daya daga cikinsu da za a wajabta aiki da ita akan kasashen da lamarin ya shafa, kawai dai maganganu ne na fatar baki. A nasa bangaren Gregor Gysi daga jam’iyyar gurguzu korafi yayi da cewar shi kansa taron ma dai ba shi akan wata turba ta demokradiyya, domin kuwa babu wata kasa ta Afurka ko Latin Amurka da aka gayyace ta shiga tattaunawar, illa kawai a matsayin ‘yan kallo, duk kuwa da yayata maganar taimako ga wadannan kasashe da ake yi.