1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sansanin gwale-gwale na Guantanamo

January 10, 2006

Wakilin DW ya kai ziyara sansanin gwale-gwale na Gwantanamo

https://p.dw.com/p/Bu2Z
Fursinoni a Guantanamo
Fursinoni a GuantanamoHoto: dpa

An dai bai wa wakilin na DW da wasu takwarorinsa ‘yan jarida cikakkiyar dama ta kai ziyara sansanin gwale-gwalen na Guantanamo, wanda Amurka ke haya daga kasar Cuba tun kafin shugaba Fidel Castro ya dare kan karagar mulki. Kuma ko da yake akan gabatar da kiran salla sau biyar a rana a sansanin gwale-gwalen, inda kasar Amurka ke azabtar da fursinonin da ta tsare ba a bisa ka’ida ba a karkashin matakin da ta kira wai na yaki da ta’addanci, amma lamarin kamar gigin barci ne ga duk wanda ya ziyarci wannan yanki. Kazalika ko da yake an ba wa ‘yan jaridar damar bincike da daukar hotuna daga sansanin, amma kuma mahukuntan sojan Amurka sun shimfida ka’idojin da suka hada har da tace hotunan da aka dauka bisa dalilai na tsaro. Kazalika sojojin na bin diddigin ‘yan jaridan tun safe har maraice. A lokacin da take kewayawa da ‘yan jaridan a wannan sansani daya daga masu tsaron fursinonin ta nuna musu wani dan karamin dakin kurkuku mai matsatsin gaske inda tace aka tsare fursinoni masu taurin kai ne a ire-iren wadannan dakuna, inda ba kome a ciki illa wasu ‘yan tarkace, sai kuma Al-Kur’ani mai tsarki da aka rarraba a dukkan dakunan kurkukun dake wannan sansani na gwale-gwale. Dangane da masu da’a a tsdakanin fursinonin kuwa su kan zauna ne a wasu zauruka da aka tanadar musu tare da wasu ‘yan kayan wasanni da kuma damar kai da komo a sansanin. Akan kuma gabatar da rahotannin abubuwan dake faruwa a kasashen da fursinonin suka fito akan wani allon da aka tanadar bisa manufa. Su dai sojan Amurka dake tsaron fursinonin ba sa kaunar jin an yi batu a game da wani gidan kurkuku ballanta na ma a tabo maganar sansanin gwale-gwale, kuma janar Jay Hodd, babban kwamandan sojojin a Guantanamo ya kan yi bakin kokarinsa wajen ikirarin cewar ba a gana wa fursinonin azaba, inda yake cewar wai ba su da wani abin da zasu boye game da halin da fursinonin ke ciki, lokacin da wani dan jarida ya tambaye shi dalilin da ya sanya har yau Amurka ta kiya kememe a game da ba wa wakilan hukumar kare hakkin dan-Adam na MDD kai ziyara sansanin na gwale-gwale. Sojojin na musunta duk wani batu na azabtar da fursinonin, amma a daya hannun ba sa yarda a ji tabakin su kansu fursinonin da lamarin ya shafa. Ga dai abin da janar Hood ke cewa:

“A hakika bani da ta cewa a game da wannan batu. Kuma a ganina kowa na da fahimtarsa iya gwargwado a game da ma’anar kalmar azaba. Kowane mutum da za a tambaya zai ba da wata amsa dabam. A baya ga haka ire-iren wadannan matakai na azabtarwa, kamar nutsar da kan fursuna a cikin ruwa har sai ya ji kamar numfashinsa zai yanke, ba shi cikin zartaswar sakataren tsaro. A takaice dai ba ni da wani abin da zan ce game da wannan batu.”