1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sarauniya ta amince da shirin fita daga EU

Yusuf Bala Nayaya
March 16, 2017

Wannan jawabi da ke fita daga bakin kakakin majalisa John Bercow ya ce Firaminista May na da dama ta fara shirin tattaunawar barin Kungiyar EU ko daga wane lokaci.

https://p.dw.com/p/2ZLlO
Großbritannien Königin Elizabeth II. eröffnet das britische Parlamentsjahr mit der traditionellen Thronrede
Hoto: Reuters/A. Grant

Sarauniya Elizabeth ta Birtaniya ta amince ga Firaministar Birtaniya Theresa May ta fara aiwatar da shirin tattaunawar gwamnatin kasar a kokari na ficewa daga Kungiyar Tarayyar Turai ta EU, matakin da ke zuwa  bayan da a yammacin Litinin 'yan majalisar suka amince da wannan yunkuri.

Wannan jawabi da ke fita daga bakin kakakin majalisa John Bercow ya ce Firaminista May na da dama ta fara shirin tattaunawar barin Kungiyar EU ko daga wane lokaci daga yanzu, ko da ya ke da fari mai magana da yawun May a ranar Litinin ya bada hasken cewa wannan mataki na sarauniya zai zo a karshen wata sai ga shi bayanan na zuwa a 'yan kwanakin nan.