Sarkin Spain na adawa da fafutikar Kataloniya | Labarai | DW | 04.10.2017

Labarai

Sarkin Spain na adawa da fafutikar Kataloniya

Sarki Felipe na shida na Spain ya soki lamirin masu rajin ballewar yankin Kataloniya tare da yin kira ga gwamnatin kasar ta Spain da ta dauki matakan da suka dace domin maido da doka da oda a yankin.

König Felipe hält Rede an die Nation (picture-alliance/Casa Real/Europa Press)

 Sarki Felipe ya yi wannan furuci ne a cikin wani jawabi mai cike da kausasan lafukka da ya gabatar inda ya zargi gwamnatin Carles Puigdemont ta yankin na Kataloliniya da taka kundin tsarin mulkin kasar da gangam ba so daya ba: 

"Gwamnatin yankin Kataloniya ta keta haddin duk wasu dokoki da tsarin demokradiyya, kana ta raba kawunan jama'a da ma haddasa tashin hankali a yankin na Kataloniya da ma Spain din baki daya"

Wannan dai shi ne karo na farko da Sarki Felipe na Shida ke nuna fushinsa karara tun bayan faruwar wannan rikici na yankin Kataloniya shekaru 40 da suka gabata. 

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da al'ummar yankin na Kataloniya ke gudanar da wani yajin aiki na gaba gari domin nuna hushinsu dangane da yadda 'yan sanda suka yi amfani da karfin tuwo wajen neman hada gudanar da zaben rabagardama a ranar Lahadin da ta gabata.  

Albanian Shqip

Amharic አማርኛ

Arabic العربية

Bengali বাংলা

Bosnian B/H/S

Bulgarian Български

Chinese (Simplified) 简

Chinese (Traditional) 繁

Croatian Hrvatski

Dari دری

English English

French Français

German Deutsch

Greek Ελληνικά

Hausa Hausa

Hindi हिन्दी

Indonesian Bahasa Indonesia

Kiswahili Kiswahili

Macedonian Македонски

Pashto پښتو

Persian فارسی

Polish Polski

Portuguese Português para África

Portuguese Português do Brasil

Romanian Română

Russian Русский

Serbian Српски/Srpski

Spanish Español

Turkish Türkçe

Ukrainian Українська

Urdu اردو