1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sarkozy a Amurka

November 8, 2007
https://p.dw.com/p/C5IV

Shugaba Nicolas Sarkozy na kasar Faransa ya tabbatarwa da majalisar Amurka cewar,kasarsa zata marawa Washinton baya a kokarin ta na yaki da shirin nuclearn kasar Iran ,da ayyukan tarzoma a Afganistan.Wannan shine karo na farko cikin sama da shekaru 10,da wani shugaban kasar faransa yayi jawabi wa hadin gwiwar majalisar dokoki dana Dottijan Amurka.Wannan dai na nunar da yadda dangantaka ta kullu tsakanin Amurka da Faransa.A wani lokaci yau din ne kuma ake saran Nicolas Sarkozy na Faransan,zai gana da George W Bush na a Mount Vernon,dake zama fadar shugaban Amurka na farko George Washinton.Anasaran shugabannin biyu zasu tabo batutuwan kasashen Iraki da shirin NUclearn Iran da kuma matsalar Dumamar yanayi.