1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sarkozy da Rudd sun kai ziyarar ba zata a Afghanistan

December 22, 2007
https://p.dw.com/p/CfGZ

Shugaban Faransa Nicolas Sarkozy ya bar ƙasar Afghanistan zuwa ƙasar Tajikistan bayan wata ziyarar ba zata da ya kai a birnin Kabul inda ya gana da shugaba Hamid Karzai. Sarkozy ya ce bai kamata gamaiyar ƙasa da ƙasa ta sha kaye a yaƙin da take yi da ta´addanci a Afghanistan ba. Shugaban ya ce Faransa tana iya kara yawan sojojinta a ƙasar. Yanzu haka dai Faransa na da sojoji dubu daya da 900 a Afghanistan. Sarkozya ya ce a cikin wasu makonni masu zuwa za a yanke shawara dangane da kara yawan sojojin. A kuma halin da ake ciki sabon Firaminsitan Australiya Kevin Rudd ya kai wata ziyarar ba zata Afghanistan inda ya gana da shugaba Karsai. Rudd wanda ya ce zai janye dakarun Australiya daga Iraqi, ya jaddada aniyarsa ta sake gina Afghanistan tare da samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a ƙasar.