1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sarkozy ya bi sahun Kouchner kan yiwuwar daukar matakin soji kan Iran

September 21, 2007
https://p.dw.com/p/BuAk

Shugaban Faransa Nicolas Sarkozy ya ce zai goyi bayan duk wani takunkumi mai tsauri da za´a kakabawa Iran saboda kin da ta yi na dakatar da aikace´aikacen ta na nukiliya. A lokacin da yake magana a wata hira da wata tashar telebijin Faransa shugaba Sarkozy kai tsaye ya zargi Teheran da hankoron kera makaman nukiliya. To sai dai ya jaddada cewa Faransa ba zata so wannan takaddamar da ake yi da Iran ta kai ga wani rikici na soji ba. Shi kuwa shugaban Amirka GWB fadawa manema labarai a fadar White House yayi cewa yana fata kwamitin sulhun MDD zai kara mastawa Iran lamba a wani yunkurin cimma wata maslaha ta diplomasiya.