1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sarrafa shara zuwa kudi a Kenya

December 14, 2016

Geoffrey Baluzi dan garin Watamu da ke Yammacin kasar Kenya ya yi nazarin gurbataccen yanayinsu saboda tulin shara dan haka da wata kungiya ta Watamu Marine Association su ke kawo sauyi.

https://p.dw.com/p/2UGXC
Porträt - Geoffrey Baluzi
Hoto: DW

Kowacce ranar Litinin, rana ce da Geoffrey Baluzi wani dan Jari Bola a garin Watamu na kasar Kenya ke bin bakin teku tare da abokan aikin sa na kungiyar Watamu Marine Association kungiyar d ake rajin kare muhalli suna karbar shara  musamman ma robobi. Kowanne dan jari bola ya na samun akalla Euro hudu kullum, Euro 16 a wata

Kenia Nairobi Lorna Rutto
Hoto: L. Rutto

Bayan karbar sharar da kuma tara ta wannan kungiyar ta Watamu Marine Association ta kan mika zuwa ga wani bangare na sarrafa shara a cikin wannan kungiya daga nan sai su ware sharar gida biyu bangaren roba mai laushi da kuma manyan robobi masu karfi, wasu kuma daga ciki akan mika su ga wata kungiya ta mata  da masu yin zayyana wadanda ke sarrafa su zuwa ga mafici da kayan wasan yara, ita dai wannan kungiya tana samun kudin shiga har Euro 7,000 a shekara.

Tare da mallakar wata na'ura mai narkar da sharar gamagari su na kuma fatan samun injin da zai rika sarrafa musu roba anan gaba,kamar yadda Geoffrey Baluzi ya kara da jaddada cewar shifa ya na ganin alamun nasara a harkar Jari Bola ganin da dama shara da ke tare a gaban teku ta ragu. Sai dai duk da haka wannan kungiya ta Watamu Marine Association mai yaki da shara ta hanyar Jari bola a kasar Kenya ta bayyana cewar har yanzu ta na da jan aiki a gabanta na wayar da kan jama'a.