1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Saudiya zata aika sojinta na kiyaye zaman lafiya zuwa Iraqi----

Jamilu SaniAugust 2, 2004

Sakatare janar na kungiyar kasahen larabawa ya ba zai yiwu sojn kasahen musulmi da za'a tura Iraqi su zauna karkashin sojin Amurka ba---

https://p.dw.com/p/Bvhb
Hoto: dpa

Koda yake a halin yanzu kasahen larabawa da sauran kasahen musulmi basa kaunar aika dakarun su na kiyaye zaman lafiya zuwa kasar Iraqi,to amman kuma a tattaunawar da sakatare janar na kungiyar kasahen larabawa Amar Mussa yayi da shugabanin kasar saudi Arabia jiya lahadi,ya baiyana cewar kasahen larabawa zasu aika dakarun su na kiyaye zaman lafiya zuwa kasar Iraqi don su maye gurbin sojin taron dangi na Amurka dake kasar Iraqi.

Kamfanin dilancin labarun kasar Saudi Arabia na SPA ya rawaito sakatare janar na kungiyar ta kasahen larabawa kasahen larabawa Mussa na cewar a hakikanin gaskiya kasahen larabawa dana musulmin duniya,basa kaunar su aika sojin su na kiyaye zaman lafiya zuwa kasar Iraqi,to amman kuma kowace daga cikin wadanan kasahe na iya aika sojin nata na kiyaye zaman lafiya zuwa kasar ta Iraqi matukar dai ta ga cewa hakan ya dace da ita.

Amar Mussa ya furta irin wadanan kalamai ne a lokacin da ya gana da yarima Abdullah mai jiran gado da kuma ministan harkokin wajen saudia Saud al-faisal a birnin Jeddah a lokacin da ya kai ziyarar aiki ta takaitacen lokaci zuwa kasar ta saudia Arabia.

Sakatare janar din na kungiyar ta kasahen larabawa Amar Mussa ya baiyana gamusuwarsa da manufar gwamnatin Saudia na aika sojinta na kiyaye zaman lafiya zuwa kasar Iraqi,inda ya ce daukar wanan mataki zai taimaka wajen ficewar dakarun mamaye na ketare dake cikin kasar Iraqi a halin yanzu.

Ya dai kara da cewar sauran kasahen larabawa dana musulmin duniya,na iya cimma manufar aika dakarun su na kiyaye zaman lafiya zuwa kasar Iraqi,da zarar saudia ta fara aika sojinta na kiyaye zaman lafiya zuwa kasar Iraqi.

Amar Mussa yayi nuni da cewar ba wai aika dakarun kasahen musulmi zuwa Iraqi keda wuya ba,abinda zai kawo cikas wajen aiwatar da wanan manufa shine karkashin wa sojin na kasahen musulmin zasu kadance a kasar ta Iraqi.

Bugu da kari sakatare janar din na kungiyar kasahen larabawa ya baiyana cewar ba zai yiwu a ce sojin kasahen musulmi sun tafi zuwa kasar Iraqi a ce sun zauna karkashin sojin Amurka fiye da majalisar dikin duniya ba.

Amar Mussa ya baiyana cewar kungiyar kasahen musulmi ta duniya ce cimma manufa game da aika dakarun kasahen musulmi zuwa kasar Iraqi.

Tun a jiya lahadi ne dai ministan harkokin wajen saudia Saud al-Faisal ya baiyana cewar dukanin sojin kasahen musulmi da za’a tura zuwa kasar Iraqi,zasu kasance ne karkashin kulawar sojin taron dangi na Amurka dake Iraqi.

A tattaunawa da sakataren harkokin wajen Amurka Colin Poweel yayi da Pm gwamnatin rikon kwarya na Iraqi Iyad Allawi,sun tatauna kann yiwar aika sojin kasahen musulmi zuwa kasar Iraqi,har ma kuma aka tsaya kann shawarar cewar kasahen dake makwabtaka da Iraqi ya kamata su aika sojin su na kiyaye zaman lafiya zuwa kasar ta Iraqi.