1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukuncin kisa ga wasu mutane hudu a Saudiyya

Yusuf BalaAugust 26, 2015

Daya daga cikin wadanda aka aiwatar wa hukuncin na kisan daga cikin 'yan kasar ta Saudiyya Nawaf al-Otaibi an same shi da laifin kisan mahaifinsa.

https://p.dw.com/p/1GLhQ
Saudi-Arabien König Salman ibn Abd al-Aziz
Sarki Salman na SaudiyyaHoto: Getty Images/AFP/S. Loeb

A ranar Laraban nan kasar Saudiyya ta aiwatar da hukuncin kisa ga wasu mutane uku 'yan asalin kasarta saboda aikata kisan kai da suka yi har ila yau ta kuma aiwatar da irin wannan hukunci kan wani dan kasar Siriya saboda kama shi da laifin fasakaurin miyagun kwayoyi. Aiwatar da wannan hukunci kuwa na zuwa ne kwana daya bayan da kungiyar kare hakkin bil'Adama ta kasa da kasa wato Amnesty International ta bayyana cewa ana ci gaba da samun karuwar wadanda ake yanke musu hukuncin kisa a wannan kasa ta Saudiyya mai ra'ayin 'yan mazan jiya.

Wannan hukunci dai ya sanya yawan wadanda aka aiwatar wa hukuncin na kisa sun kai mutane 127 cikin wannan shekara kadai a kasar ta Saudiyya; idan aka kwatanta da mutane 87 da aka halaka a shekarar 2014 kamar yadda wata kididdiga ta kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP da ya tattaro bayanai daga ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar ta Saudiyya ta nunar.

Daya daga cikin wadanda aka aiwatar wa hukuncin na kisan daga cikin 'yan kasar ta Saudiyya Nawaf al-Otaibi, an same shi ne da laifin kisan mahaifinsa da bindiga shima an yi masa hukuncin kisan a ranar Laraban nan a yammacin birnin Ta'if na kasar ta Saudiyya.