1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Saudiyya ta ba da izinin bude gidajen sinema

Gazali Abdou Tasawa
December 11, 2017

Mahukuntan kasar Saudiyya sun ba da izinin sake bude gidajen sinema da ma sauran wuraren shakatawa a kasar bayan shekaru 35 na haramci.

https://p.dw.com/p/2p9QL
Saudi-Arabien Riad Filmfestival
Hoto: Getty Images/AFP/Stringer

Mahukuntan kasar Saudiyya sun ba da izinin sake bude gidajen sinema da wasu wuraren shakatawa da nishadantarwa a kasar bayan shekaru 35 na haramci. Ofishin ministan raya al'adun kasar ta Saudiyya ne ya sanar da hakan a wannan Litinin a cikin wata sanarwa da ya fitar inda ya ce matakin zai soma aiki a farkon shekara ta 2018, amma tun yanzu gwamnatin za ta soma bayar da lasi ga masu bukatar bude gidajen sinemar. 

Gwamnatin kasar ta Saudiyya na son yin amfani da sabon salon mulkin da yarima Mohammed Ben Salmane ya kaddamar domin farfado da matakan raya al'adu ta hanyar bude gidajen shakatawa na kade-kade da wake-wake da na wasanni da ma na sinema wannan kuwa duk da adawar da matakin ke fuskanta daga masu ra'ayin rikau a kasar wadanda ke kallon wadannan wurare a matsayin na alfasha.